NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

GAREKI UWAR GIDA......KOWACCE MATAR AURE. TA DAURE TA KARANTA domin amfaninki💐💐💐 *SIRRIN YA MACE Group *💐💐💐

*admin maijidda bello *✍️

Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta adakin aure, awannan zamanin da muke ciki, ta gode ma Allah. Ba don komai ba, idan ta duba zata ga wasu ‘yan-mata irinta, sunfi ta kyawun halitta da iya ado, amma har yanzu basu samu mijin aure ba.

Don haka zai fi alkhairi agareki ki Qudurce acikin zuciyarki cewa GIDAN MIJINKI NAN NE WAJEN NEMAN ALJANNARKI.
Ki rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da tsaftar jikinki da tsaftar Muhallinku. Kuma ki zama ko yaushe ashirye kike domin biyan bukatar mijinki ko da bai nema ba.
Ki kiyaye MUGAYEN QAWAYE… Ba zasu rasa yi miki hassada ba. Tunda ke kin samu miji, su kuwa basu samu ba… Dole suyi miki hassada.


Ki kiyaye sirrin mijinki, kar ki gaya ma kowa.. Musamman ma kawayenki zasu so suji abinda yake faruwa.. Don haka kar ki gaya musu.
Idan kuna da ‘ya’ya to ki kula dasu, ki kula da tsaftarsu. in ma ‘ya’yan kishiyarki ne, to ki kula dasu kamar yadda zaki kula da ‘ya’yanki.
Ki kiyaye dukkan amanonin mijinki. musamman ma iyayensa da ‘yan uwansa da dukiyarsa.

*admin maijidda bello *✔️

+2335061_______505
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts