NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

FA'IDODIN HABBATUS SAUDA { admin maijidda bello}










FA'IDODIN HABBATUS SAUDA

{ admin maijidda bello}

1. MAGANIN SAURO DA SAURAN QWARI MASU CUTARWA: asamu garin Habbatus sauda, aturarashi daidai Misali. Insha Allah duk wasu Qwari masu cutarwa kamarsu Kyankyaso, sauro, tsaka, Qadangare, Kunama, duk zasu fice daga dakin.

2. Irin yaran nan wadanda zaka ga an haifesu basu da lafiyar kwakwalwa sosai, wato MUGAFFAL kenan. Asamu Man habbatus Sauda atofa Fatiha 1, ayatul kursiyyu 11, Qul huwallahu da falaki da nasi Qafa 3 sannan arika bashi yana shan cokali guda kullum, kuma arika shafa masa duk jikinsa. Musamman ma kayinsa. Insha Allahu zai samu gyaruwar Kwakwalwa da kuma basira.

3. MATA MASU JUNA BIYU: asamu garin Habbatus Sauda cokali 7, citta da kanunfari cokali 2, ahada cikin zuma kofi guda da rabi. Arika shan cokali 1 safe da rana da yamma.

Insha Allahu zata samu kuzari da Qarfin jikinta. Kuma zata samu kariya daga cututtuka da ita da jaririnta. Kuma zata samu saukin nakuda.

4. FITAR MAZIYYI: samarin da suke fama da matsalar fitar maziyyi ba bisa qa'ida ba, idan suna shan Man habbatus Sauda ko garinta tare da zuma insha Allahu zai dena zubo musu ba bisa ka'ida ba.

5. TSUTSAR CIKI: habbatus Sauda tana maganin ciwon kai idan ana shafawa. Tana maganin ciwon ciki idan ana shanta sosai. Kuma tana narkar da Tsakuwar Qoda idan ana shanta da zuma

6. CIWON HAQORI : achudanya Man Habbatus Sauda tare da Ma'u-Khal daidai gwargwado, arika kurkure baki dashi. Insha Allahu hakorin zai dena ciwo.

7. RHEUMATISM : asamu Man Habbatus Sauda na kampanin hemani ko kuma 'dan Misra, adumamashi sannan arika shafawa ajikin Qafar, ana matsawa. Sannan arika shan Zuma wacce aka gauraya da garin Habbatus sauda cokali guda kullum kafin akwanta barci da minti 15.

8. CIWON IDO, CIWON KUNNE: asamu man habbatus Sauda atofa fatiha 7 Qul huwallahu 7 da falaki da nasi 3, sannan atofa ayatush Shifa'I. Sai arika 'digawa acikin Kunnen ko kuma idon da yake ciwo. Insha Allahu za'a samu waraka.

9. CIWON NONO, CIWON DAJI : Asamu man Habbatus Sauda Cokali 12 ahada tare da Man Jirjeer cokali 12. Man Zaitun cokali 12 Man Raihan shima haka.

Ki tsoma yatsanki aciki sannan ki karanta:
Fatiha 7,
ayoyi 4 na farkon suratul Baqarah.
Ayatul kursiyyi tare da ayoyi 2 na bayanta.
Ayoyi 3 na karshen suratul baqarah.
Ayatush Shifa'I.
Qul huwallahu da falaki da naasi.

Sannan ki karanta wannan addu'ar:

"YAA KASHIFADH-DHURRI INNEE MASSANIYADH-DHURRU WA ANTA AR'HAMUR RAHIMEEN" (11).

Salatun Nabiyyi (saww) daidai gwargwado.

Sannan ki raba wadannan magungunan gidan biyu: kashi na farko ki rika zubawa acikin dukkan abincin da zaki ci. Kashi na biyu kuma ki rika shafawa. Insha Allahu zaki ga aikin Allah da gaggawa.

Hakanan masu fama da cutar Paralysis da duk wani nau'in cututtuka masu wuyar Magani. Suma idan sukayi wannan hadin zasu ga waraka Bi'iznillahi.

10. MAGANIN KUTURTA (LEPROSY) ALBARAS:

Asamu :

1. Ma'u Khal wanda aka surkashi kadan.
2. Garin Habbatus Sauda.
3. Garin Lalle.
4. Fatar Hawainiya nikakkiya.

Adebi cokali 3 na kowanne daga ciki agaurayasu tare da Ma'u khal acikin roba. Sannan arika shafawa awajen da kuturtar ta bayyana, kafin akwanta barci. Sai awanke da safe. Sannan arika barin rana tana dukan wajen da hantsi. Insha Allahu za'a samu waraka.

11. MAGANIN DIABATES (CIWON SUGAR) :

* Garin H/sauda kofi guda.
* Garin Shuwaka Babban cokali 1.
* Garin Habbur Rashad Rabin Kofi.
* Garin Rummaan Kofi guda.
* Bawon Karnab Kofi guda. (Shi wannan ba dole bane)
* Garin Hiltit cokali 1.

Ahadasu gaba daya agauraya sannan arika zuba cokali guda acikin madara ana sha kullum da safe kafin akarya (breakfast).
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts