NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

ABUBUWAN DA YA KAMATA MAI JUNA BIYU KIYI A WATANNI UKUN KARSHE (3RD Trimester period)Yea
ABUBUWAN DA YA KAMATA MAI JUNA BIYU KIYI A WATANNI
UKUN KARSHE (3RD Trimester period)
. .
1. Dole ne ki lakanci motsin jaririnki sbd jarirai da yawa
kowanne nada yanayin yadda yake kwanciya da tashi. Saboda
haka duk sanda Kika lakanci motsin babynki to idan har ya
canza yanayi zata fahimta sai ta je taga midwife ko likitanta.
2. Ki zamo cikin Sani dangane da alamomin dake nuni da
matsala dangane da mai juna biyu kamar (jijjiga, Hawan jini,
zazzabi mai zafi, Ciwon kai mai tsanani, zubar jini, Kumburi,
doguwar nakuda fiye da yini guda wato awa Sha biyu. ds,
3. Cin abinci mai inganci Kuma a wadace, wato cin abinci
mai Gina jiki hade da Karin jini fruits, vegetables & proteins
(alayyahu, naman kaza, kifi, orange juice, etc.
4. Kike motsa jiki kina yin stretching domin hakan zai sa ki
jin dadi hade da dena jin wuyar zama da tashi da kyar cikin
nishi, Denajin Ciwon kafafun, da Kuma rage jin Ciwon baya da
kugu.
5. Kamar yadda cikin ke dada girma abune mai kyau
maigidanki ki kwanta ya rika miki tausa yana mammatsa miki
jikinki tare da tudun cikin Shima ya rika dan daddanna miki a
hankali gefe da gefe.
6. Kike magana da jaririnki domin yana jinki inkikai magana
a wadannan watanni biyun na karshe, hakan zai kara sa
dangantaka da shaquwa tare da fara sabawa da jin muryarki
fiye da ta kowa.
7. Yana da kyau ki fahimci Matakan nakuda zuwa haihuwa
domin sanin nakudarki ya zata kasance idan kinji kin fara don
a daukar miki Matakan da suka dace.
8. Sannan yana da kyau mai juna biyu da maigidanta su
tsara inda zata ta haihu asibiti ko kuma wata kwararriyar
ma'aikaciyar jinyar da zata kasance tare da ita in haihuwa tazo
domin bata kulawa.
9. A tanaji kayan sawar baby masu kyau gami da bada
kariya da Kuma dacewa da lokacin haihuwa walau lokacin
sanyi ko zafi, tare da tanadar mayuka da powder da bazasu
cutar da fatar jaririn ba.
10. Ki gyara da shirya jakar tafiya asibiti haihuwa ki aje
domin da lokacin yayi saidai a dauka atafi batare da 6ata
lokaci ba.
11. Kike samun bacci isashshe kina Yi.
12. ki rage aikace aikace da yawa wadanda zasu jijjiga ki
fiye da kima.
13. Ki binkice ko ki karatu na musamman dangane da
yadda ake kula da jarirai (baby care) domin jaririnki ya zamto
mai lafiya, tare da daukarsa rigakafi.
14. Ki shirya domin aikin shayarwa sannan tare da sanin
yadda ake bada nonon.
15. Ki sami wata wacce kuke watanni daya juna biyunku
suke kuke tattauna wa tare da kara fahimtar da kanku abunda
wata Kila batasan hakan ba sai yanxu..
SAMUWAR ISASHSHEN RUWAN NONO
Babban abunda ke Qara ruwan nono shine dagewa da cigaba
da baiwa yaron nonon akai akai duk da kan-kantarsa ruwan
nonon domin hakan shike lausasa jijiyoyin dake dauko nonon
suke sashi yana tsatstsafowa ahankali sai aga ya Karu.
- Sai Kuma abincin; hade juice na karas Ana Sha ko yawan cin
carrot din na taimakawa.
- Yawan shan abarba.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts