NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

YANDA ZA'A MAGANCE BAKIN HAMMATA

Hammata na daya daga cikin sassan jikinmu da ke da yawan fitar da zufa, kuma wanda ba shi da wuyar fara wari, al’amarin da ke matukar baiwa wasu daga cikinmu takaici.

A don haka ne wasu ke amfani da turarikan hammata wadanda suka yi alkawarin za su hana zufa.

Sai dai duk da cewa ana amfani da su, mutum zai fuskanci cewa hakan bai hana hammatar ta yi wari ba, sai dai warin ya hadu da kamshin turaren.

Dalili shi ne; shi kansa zufa ba shi ya ke haifar da warin hammata ba, wannan alhakin na kan kwayoyin ‘bacteria’. Hasali ma zufa na dauke da wani sinadari mai suna ‘Dermicidine’ wanda ke hana wadannan kwayoyi masu sanya wari su shiga jiki.

warin hammata

Sai dai wadannan turarikan da muke amfani da su na toshe kofofin yin zufa ne, su hana jiki fitar da shi, al’amarin da ke dakile aikin da wannan sinadari ke yi ga jiki. Idan hakan ta faru, sai kwayoyin ‘bacteria’ su samu gurin zama su yi ta yaduwa, hammata kuma ta yi ta wari.

Turarikan hammata wanda ake kira ‘Deodorant’ ko ‘Anti-perspirant’ a turance na dauke da sinadarai masu hatsari ga lafiyar jiki kamar su ‘Aluminium’ wadanda ke shiga jiki ta kofofin fata.

Abunda ake amfani da shi a Maimakonsu
Akwai dan itace guda daya da ya buge duk wani turaren hana warin hammata da ke kasuwa wajen karfin aiki. Wannan dan itace ya na nan birjik a kasuwa.

Shi wannan dan itace ba ya hana zufa, saboda zufa na da mauhimmanci ga lafiyar jiki. Sai dai kawai zai hana kwayoyin sanya warin nan katabus, ta yadda ba za su samu sukunin yin abun da suka saba ba yi ba.

Wannan dan itace shi ne Lemon tsami.

lime-e1475803616257

Ana yanka shi gida biyu bayan an yi wanka, sai a shafa shi a hammata, a barshi ya bushe, sannan a sanya riga. Shike nan.

Sinadarin ‘Citric Acid’ da ke cikin Lemon tsamin zai sa hammata ta yi fes tana kamshi mai dadi na tsahon lokaci, sannan zai hana tsirowar kwayoyin ‘bacteria’ masu sanya wari wadanda ke shiga jiki ta hammata.

sannan kuma yana kara hasken hammata a sakamon wasu sinadarai da ke cikin sa dake kara hasken fata, maimakon ya sanya hammata ta yi baki kamar yadda wasu turarikan ke yi.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts