NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

YANDA AKE RING DUNUT 🍩🍩🍩


Posted maijidda bello- Filed in Girke-Girke - #abinci #girke-girke #donut #yadda ake donut -
Yadda ake Donut
Abubuwan hadawa
Falawa kopi 3
Bota 1
Kwai 3
Mangyada
Suga rabin kofi
Gishiri rabin cokali
Yeast cokali daya
Baking hoda cokali 1
Yanda ake hadawa
Da farko zaki tankade fulawarki a kwano mai fadi.
Sai ki sa yeast da baking hoda ki juya, sai ki sa bota ki yi ta juyawa ya hadu da fulawan sosai.
Sai ki fasa kwanki ki zuba ki juya ya hadu da fulawan.
Sannan sai ki zuba suganki a ruwan dumi ki juya sai ki zuba a fulawar ki kwaba da dan gishiri.
Idan yayi sai ki rufe ki sa a rana yayi kamar minti arba'in.
Sai ki duba idan ya tashi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mangyada.
Sai kuma ki kawo gwangwanin madara na ruwa don ki samu yayi rawun sai ki sa a paranti ki dinga murzawa kina sa wannan gwangwanin kina fitar da rawun din donut dinki, kuma ki na sawa a mai kina soyawa, hakan zaki yi tayi harki gama.
Na gode.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts