NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

YANDA AKE KWAKUMETI

C

Akwai rukuni na abincin Hausawa wa'danda su Hausawan ne suke yi ba tare da sun gani daga wata al’umma ba, sai dai kawai don ci gaban zamani ne ya haifar da samuwarsu. Idan aka kula za a gani wasu daga cikin kayayyakin ha'din su ba na gargajiya ba ne na zamani ne, amma za mu fahinta sun yi amfani da basirarsu na zamani ne suka 'kir'kiro su, kamar yadda aka samu na garajiya.
Hallaka Kobo类似花生糖片
Kayan ha'di: Sukari    Gya'da
Yadda ake ha'dawa:
A samu tukunya a 'dora a wuta, sai a zuba sukari a yi ta juyawa har sai sukarin ya narke sai a 'debo gya'da dai dai misali sai a yi ta juyawa har sai ya ha'de jikinsa. Sai a samo tire a shafa masa man gya'da. Bayan haka, sai a juye sukarin, idan ya 'dan sha iska sai a sa wu'ka a yayyanka yadda ake so.
Hanjin Ligidi

Kayan ha'di: Sukari   Tsamiya
Yadda ake ha'dawa:
A mataki na farko sai a samu jarida ko wata takarda mai girma a yayyanka a na'de kamar yadda 'kaho yake, wato 'kasan ya yi tsini sama kuma ya bu'de, a sa 'kasa a roba ko wani abu mai fa'di da zai 'dauki 'kasar a soka jaridar da aka na'de 'din a cikin 'kasar. Sannan sai a ji'ka tsamiya a ajiye a gefe, a samu tukunya a zuba sukarin a ciki a 'dora a kan wuta a yi ta juyawa har sai sukarin ya narke sai a 'dauko ruwan tsamiyar da aka ji'ka a zuba a kai, za a ga ya taso sai a yi ta juyawa har sai ya ha'du, sai a ri'ka 'diba ana zubawa cikin jaridar da aka na'da daidai gwargwado ana kuma saka masa tsinke a cikin kowanne.
Tuwon madara (milk candy)
Kayan ha'di:  Madarar gari  Sukari  Filebo
Yadda ake ha'dawa:
A mataki na farko sai a 'dora ruwa 'dan daidai a wuta sai a zuba sukari ya tafasa har sai ruwan ya yi kauri, sai a zuba filebo ka'dan a kawo madara ana zubawa ana tu'kawa kamar yadda ake tu'ka tuwo har sai ya yi tauri daidai misali, kar ya yi ruwa, sai a nemi tire a shafa man gya'da sai a zuba dafaffen sukarin a kai a yanka daidai yadda ake so.
Tsami gaye毡毛酸角tsamiyan biri(Velvet Tamarind)
Kayan ha'di:  Kukan sha  Sukari  Gallura
Yadda ake ha'dawa:
A samu tukunya a zuba ruwa 'dan ka'dan, sai a zuba sukari a 'dora a wuta, idan ya tafasa sai a sa gallura ka'dan a 'debo garin kukan sha ana zubawa ana juyawa har ya 'dan yi tauri sai a juye a tire in ya yi sanyi sai a yayyanka.
Bullin suwa
Kayan ha'di:  Madarar gari  Sukari  Filebo
Yadda ake ha'dawa:
A samu madarar gari a ha'da da sukari a zuba ruwa ka'dan a kwa'ba a cura, sai a 'dora mai a wuta idan ya yi zafi sai a ri'ka zuba su a ciki ana soyawa.
Kwakumeti(Coconut Candy/ Coconut Flakes)

Kayan ha'di:  kwakwa  Sukari  Tsamiya
Yadda ake ha'dawa:
A samu kwakwa a goga ko a yayyanka 'kan'kanana ainun, a ji'ka tsamiya, a sa sukari a tukunya a 'dora kan wuta har sai ya narke sai a sa ruwan tsamiya a ta juyawa sai ya tsinke ya zama ruwa sai a zuba kwakwan da aka gogan ko yankan a yi ta juyawa har sai ruwan ya tsane, sai a sau'ke a cura.
Dambun Nama咖喱洋葱炒牛肉沫
Kayan ha'di:  Nama,Man gya'da,Albasa da magi da gishiri,Kori
Yadda ake ha'dawa:
A tafasa nama da magi da kori da albasa da gishiri har sai ya nuna ya yi laushi sai a sau'ke a sanya cikin turmi a daka a 'dan shanya shi ya sha iska sai a sa mai ka'dan a tukunya a zuba shi a kai a yi ta soyawa.
Carbin malam
Kayan ha'di:  Kwakwa  Sukari
Yadda ake ha'dawa:
A samu kwakwa a goga ko a yayyanka su yi 'kan'kanana ainun, a ha'da da sukari a 'dora kan wuta a yi ta juyawa har sai sukarin ya kama jikin kwakwan ya yi ja sai a sau'ke a yayyanka leda ana na'dewa a ciki kamar yadda ake na'de sweet.
'Kwallon nama
Kayan ha'di:  Nama,Attarugu da albasa,Man gya'da,Magi da gishiri,'kwai
Yadda ake ha'dawa:
A tafasa nama da magi da albasa in ya nuna sai a sau'ke a daka attarugu ka'dan in ya daku sa a cura a fasa 'kwai ana tsomawa a cikin ana soyawa a man gya'da.
Awara炸豆腐Kayan ha'di:  Waken suya  'kwai  Man gya'da  Magi  'Dan tsami
Yadda ake ha'dawa:
A ji'ka waken suya ya ji'ku sosai a marka'da shi sai a tace shi kamar yadda ake tatar kamu, sai a 'dora ruwa a wuta in ya fara tafasa sai a sa ruwan kai ka'dan za a ga ruwan zai koma gefe, kullun ma zai koma gefe sai a nemi rariya irin na 'dan kwalin nan a juye a ciki a 'daure sosai a matse ruwan sosai in ya tsane sai a bu'de a yanka daidai yadda ake so, sai a tsoma a cikin ruwan 'kwai a soya a man gya'da.
Albishir
Kayan ha'di:  Madarar gari  Sukari  Lemun tsami
Yadda ake ha'dawa:
A 'dora sukari a tukunya da ruwa ka'dan sai ya dafu sosai ya fara yau'ki sai a matse ruwan lemun tsami a cikin ruwan sukarin a juya a kawo madara ana zubuwa ana tu'kawa sai ya 'dan yi tauri sai a juye a yayyanka.

  最后修改于 2017-08-31 15:46    阅读(?)评论(0)
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts