NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Yadda ake miyar Loni na gargajiyar Mumuye

Miyar Loni" dai wata shararriyar miyar gargaji ce ta Mumuyawa wanda suke yin ta lokaci zuwa lokaci.A saudayawa yan'kabilar Mumuye na "miyar Loni" ce a lokacin shagulgula, irin su; biki, suna, taron gargajiya da dai sauran su. A bisa al'adar Mumuye in zai yi bako ko bakuwa, ko kuma kabi a kan yi wa bakon ko bakin tuwon doya da "miyar Loni" don karramawa. Ita dai "miyar Loni" miya ce da ta shahara a wajen kabilar Mumuye, don kuwa duk mace da aka aureta in bata iya wannan miyar ba toh, da sauran ta.A bayyanin da tayi min, wata yar kabilar Mumuye wacce ta shahara wajen hada miyar mai suna, Faiza Yusuf Bitako ta min bayanin yadda ake hada wannan miyar.Da farko dai ta bayyana min kayan hadin "miyar Loni" kamar haka;Soyeyyar Gyada
Toka
Daddawa
Citta
Barkono
Nama (Kaza ko Kifi)
Kanun-fari
Masoro
Maggi
Gishiri
Albasa


Yadda ake hada miyar;Hadin miyar dai ya danganta da yadda ake bukatan yin shi, ma'ana idan da Kaza ne, toh mai miyar nada bukatan tafasa kazar ta tare da Maggi, Gishiri, Albasa da sauran kayakin yaji. Bayan naman ya tafasa ya kuma yi laushi, sai a kara ruwa kadan a tukunyar miyar da kazar ke ciki sai a daka daddawa, barkono a zuba, sai kuma a samo markadeddiyar soyeyyar gyada a zuba, sannan sai a samo tokah a zuba dai-dai da yadda ake so, sannan a samo Maggi, da Gishiri a zuba, sai a bar shi na tsawon mintuna goma zuwa sha biyar, sai a motsa a sauke.Uwar-gida kar ta manta kayayyakin hadin miyar irin su gyada da tohka sune ginshikin miyar, kuma sukan iya yiwa miyar illa in uwar gida bata kula sosai ba, yana da matukar kyau tasan irin yawan miyar da take bukata don tasan yawan kayakin hadin da take da bukata.Kamar dai yadda nayi bayani da farko ana iya yin miyar Loni ba sai da Kaza ba, illa dai a gargajiyance tun da akasari miyar ana yin ta ne lokaci zuwa lokaci musamman don karrama baki, toh anfi yin ta da Kaza. Sai dai kuma ana yin ta har ila yau da Kifi amman busheshe kawai. Don in uwar-gida tayi amfani da danyen kifi toh, zai iya lalata miyar saboda yanayin shi.Idan da Kifi uwargida zata yi miyar toh, da farko ana bukatan ta da ta gyara Kifin indan banda ne ta kuma wanke shi da ruwan zafi, sannan ta dora ruwan miyan ta da dakeken daddawa da sauran kayakin yajin ta ta zuba, sannan ta barshi na sauwon mintuna, in ya tafasa sai ta zuba markadaddiyar soyeyyar gyadar ta sannan ta zuba toka ta motsa sannan ta sanya Maggi da Gishiri sannan ta zuba kifinta a karshe.A takaice dai haka ake yin "miyar Loni" sai dai kuma ya fi dadi in aka ci shi da tuwon doya. Sai dai ba dole bane hakan. Har ila yau an fi son uwar-gida tayi amfani da tukunyar tabo wurin yin miyar a maimakon na dalma ko karfe.

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts