NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

YADDA AKE HADA SOYAYYIYAR SHINKAFA MAI ABARBA DA






GIRKINKI SIRRINKI: Tare Da Maijidda bello

Yadda Ake Hada Soyayyar Shinkafa Mai Abarba Da Gyada

Kayan Da Za Ki Tanada

1. Shinkafa

2. Naman kaza

3. Soy sos

4. Albasa da tafarnuwa

5. Danyen tattasai da koren tattasai da attaruhu

6. Karas

7. Kwai

8. Abarba

9. Fis

10. Gyada

11. Mai

12. Sikari

13. Busashshen inibi

14. Gishiri da magi

15. Kori

Yadda Za Ki Hada

Ki sami naman kazarki wajen da yake da tsoka, domin tsokar ki ke bukata ki wanke shi sosai ki zuba masa soy sos ki rufe da leda ki saka a cikin firinji ya yi awa biyu zuwa uku, ki tabbatar soy sos din ya shiga jikin kazar sosai. A gefe kuma kin dafa shinkafarki da ruwan abarba, amma ba dahuwa ligif ba, sai ki kawo mai ki zuba a kasko, idan ya yi zafi sai ki kawo naman kazar nan ki soya, idan ya soyu sai ki zuba yankakkiyar albasa da tafarnuwa da jajjagaggen tattasai da attaruhu da yankakken karas da koren tattasai da gishiri da magi da sikari dan kadan da kori ki soya su.

Idan ya soyu sai ki kawo kwai ki zuba a kai kina juya a hankali, kwan yana soyuwa kina dagargaza shi da cokali kina kara juyawa. Sai ki kawo shinkafar da kika riga kika dafa ki zuba a cikin nama da tattasan da kika soya da yankakkiyar abarba da busashshen inibi da fis ki ringa juyawa a hankali har zuwa minti uku ko bakwai. Sai ki zuba gyada ki cigaba da juyawa na minti daya. Sai ki cire daga kan wuta ki dandana ki tabbatar komai ya ji. Idan kin sauke kina iya dan kara ruwan abarbar kadan a cikin shinkafar ki juya

ABIN LURA

Danyar gyada za ki samu, ki bare ta ki soya ta sama-sama, haka kuma soy sos yana daya daga cikin muhimman kayan girki da mutanen kasar Sin suke amfani da shi, kamar dai yadda muke amfani da daddawa a miya, Uwargida kin san dai idan babu daddawa a miyar kadi sunan wannan miya lami, to su ma haka wannan soy sos din yake a wajensu. Asha dabge lahiya!

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts