NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

VAGININAL INFECTION 👇👇👇

VAGININAL INFECTION
👇🏾

VAGINAL INFECTION : Wata cutace da mafiya yawan jama'a suna kiranta da Vaginal Infection, masana kiwon Lafiya suna kiranta (Vaginitis) sabida wannan matsalar tana addabar gaban mace . Amma a Hausance ana kiranta da Ciwon Sanyin Mata.

Wannan cutar wassu kwayoyin cutane Irinsu Bakteriya, Fungus , Virus massu illartarwa su suke kawo shi .

Babban Mutum sai iya kamuwa da shi haka yara ma zasu iya kamuwa da wannan cutar.

Ba wai kawai ta hanyar jima'i ake daukan wannan Infection ba ka kadan saga hanyoyin :

1- Amfanida kayan aiki ba tareda am tsaftace shi ba lokocin haihuwa ko wanke ciki.

2- Tsaftace Gaba ta hanyar amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta.

3- Cusa hannu ko yatsa a gaba.

4- Amfani da wandon wata musamman pant .

5- Barin wadon yadauki datti (pant )

6- Rashin canxa pad akai akai lokocin al'ada .

KADAN DAGA CIKIN KWAYOYIN CUTAR DA SUKE KAWO WANNAN MATSALAR :

1- Bacteria Vaginosis : wannan wani kwayar cutace dake rayuwa cikin farji yakan haddasa matsalar Sanyin mata .

2- Candidiasis : wannan wata kwayar cutace Wanda yake haddasa Sanyin Gaba. Wadannan kwayoyin cutar suna zama cikin farji kuma basu cika cutarwa ba, wadannan kwayoyin cutar suna son waje mai gumi domin su girma dan yaduwa.

3- Trichomonas Vaginalis : wannan itace wacce take yaduwa ta hanyar jima'i. Ita wannan kwayar cutar parasite ce take kawoshi .

4- Irritation Vaginitis : ita wannan ana kiranta da Allergic , wassu abubuwanda jikin mutun bai daukesu ba, anasamunsa wajen amfanida kamar su condom, sabulu , ko maganin shafawa.

ALAMOMINTA :

1- Kuburin gaba
2- Canxa Launin gaba zuwa Ja.
3- Kaikayin gaba
4- Warin gabs
5- Kurajen gaba
6- Zubar da Farin ruwa a gaba.
7- Zafin Lokocin Jima'i
8- Zafin Fitsari.

YADDA MACE ZA TAKARE KANTA DAGA VAGINAL INFECTION:
👇🏾
1- Kada a Tsaftace Gaba Da Sabulai masu Kashe Kwayar Cuta : A cikin Farji akoi wassu kwayoyin bakteriya wadanda basa cutarwa kuma sunada amfani , amfaninsu shine suna taimakawa wajen bada kariya ga Farji , sai kaga wassu matan sukan wanke Farji da Sabulu ko detol haka , wadannan abubuwanda ake amfani wajen wanke farji yakan kashe bakteriya masu amfani na Farji , Sai masu cutarwa su samu daman shiga. A kiyaye wanke Farji Da Sabulu dakuma wadansu abubuwa Wanda bamusan Kansu ba.

2- A Tsaftace waduna : Amfani da wandon pants , wassu matan sukan bar wandonsu yayi datti , Barin datti ko amfani pant masu datti yakan bawa kwayoyin cuta daman shiga Farji.
A Tsaftace wanduna.

3- wajen wanke bahaya mafi yawa mata sukan dauki kwayar cutar da take dubura zuwa Farji, wanda basa yiwa dubura illa amma sukan yiwa Farji illah.
Shawara shine afara wanke Farji kafin a wanke dubura.

4- amfani da pants na wassu , ta yiu wacce kuke amfani da pants daya tanada cutar Sanyi idan kinyi amfani da nata kema zaki iya dauka.
Sai a kiyaye.

5- mutun yakan iya daukan wannan cutar lokocin saduwa da namiji idan namijin yana dauke dashi , hanayar Mariya itace amfanida Condom lokocin saduwa.

6- A kiyaye amfani da magungunan gargaji musamman Wanda ake cusa su a gaba , suna taimakawa wajen samun kwayoyin cuta .

MESA KORAFIN RASHIN WARKEWA YAYI YAWA ? :

1- Idan Namiji da Matar sa suna dauke da wannan cutar , abinda ya dace dukkansu biyu za sufara shan magani , bawai matar kadai ba , muddin data data cikinsu ne yake shan magani akoi matsala .

2- Duk matar da aka daurata akan magani duk zanda ta cire wandonta yakamata ya wanke ta da antiseptic kafin ta maido wannan shina yana taimakawa wajen warkewa .

3- Idan akaci gaba shan magani kuma ba'a kiyaye wassu hanyoyin da suke kawo wannan cutar ba shima akoi matsala sosai .
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts