NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

TUKUNYARKI SIRRINKI...........TUKUNYAR KI SIRRIN KI1-Gwada amfani da maggi star dan samun danɗano mai daɗi

2-Rage yawan gishiri a miya yana taimaka mana wajan rage cututtuka da hawan jini gishirin da aka saka a sulale ya wadatar a miya sai dai a kara maggi.

3-ki samu roba mai kyau ki jiƙa kanwa dan amfani yau da kullum ba sai kina zuba garinta tana ɓata abinci"¿ saboda kanwa bata rabuwa da kasa

4-idan zaki soya manja bayan kin zuba albasa tai laushi karki barta ta ƙone sai ki ɗiga kanwa a ciki yana bada danɗano mai daɗi

5-soya albasa da citta da garlic sama-sama suyi laushi kafin kiyi sauce ko stew, suna bada kamshi a girki.

6-ba lallai kullum sai kiyi jar miya ba,dunga bada sauyi dan iyalanki,zaki iya yin yar sauce,albasa,garlic citta,koran tattasai ,attaruhu,tumatur,
Zaki iya zaɓar yau kiyi amfani da wannan gobe ki sake wata saffur ,yau kinyi da carrot,ko cabbage ko alayyahu.ko kuma ki dan chopping potatoes dinki dasu albasa da carrot attaruhu ki haɗa sauce,barin aci da couscous ko rice duk dai abin da kike so.

7-wake da shinkafa ba lallai sai kullum kinyi da mai da yaji ba ko da miya,zaki iya soya manja kiyi chopping albasa da attaruhu ki soya sai maggi da kayan kamshi.
Ko kuma kisa gasashan kifi titus ki ɓare kisa aciki idan kina bukatar local maggi wato daddawa itama kisa kaɗan sai alayyahu !
Zaki iya ci da wake da shinkafa ko doya

8-idan kika markaɗa garlic tare da mai sai ki samu roba ko kwalba ki zuba,amma ba'a saka ruwa zata daɗe kina amfani da ita batare data lalace ba,ko garlic da black pepper da mai,ana ajiyewa ya jima bai komai ba.

9-idan lokacin ganye yazo kamar calary ko Parcely ko curry leaves ko mint ko lemon grass ,ki yanka ki shanya awaje marar rana awa kaɗan ya bushe sai ki samu mazubi mai kyau ki adana dan amfanin gaba.


10-masara idan aka surfa sai ajiƙa ta kwana bayan kin shanyata ta bushe sai ki haɗa da rogo irin na ɗan wake akai miki niƙa ki tankaɗe sai tuwo,anan ma zakiga sauyi zai laushi kuma bazai tauri ba sai santsi suluf

11-idan zaki dafa wake zalla dafashi a pressure pot Kisa dan sugar da gishiri zai baki danɗano mai ɗadi kamar na gwangwani barin ya danyi ruwa-ruwa

12-doya idan zaki dafa sa mata dan sugar da gishiri ga mai lafiya tana dadi

13-yana da kyau alura da kayan soye -soye ba'aso abarsu suyi kurmus ,a ido babu kyan gani a baki ba daɗi a jiki ba amfani.

14-ko kunsan babbaka wuta a girki ba shine sauri ba saima ɓata girki yasa yai kauri, wuta saisa saisa shine abinci zai dahu da kyau,sannan idan ya kusa sai a rage wuta dan ya karasa nuna da tsotsiwa.

15-kamar yanzu da ba'a rashin wuta,zaki iya ajiye kayan amfanin girki a deep freezer
kamar kuka,daddawa yaji
albasa mai lawashi,
danya ko bushashiya dadai sauran su,yadda bazasu chanja launi ko danɗano ba
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts