NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

TARBIYAR BAHAUSHE 👌TARBIYYAR BAHAUSHE.
!
!
!
!
!
!
!
Da wani yammaci ina kwance akan kujera a falona sai na jiyo hayaniya da ihu daga makotana,
da fari na yi biris domin na san gidan akwai mutane da yawa a cikinsa,
idan ta raya musu suna hirar su har da Shewa,
amman sai na ji abin na kara karuwa har da murya maza,
wannan ya tabbatar min lallai wani abu ne ke faruwa, don haka na mike cikin hanzari na fada gidan.
.
Gidan ya cika dankam da jama'a yara da manya, da kyar na iya kutsawa na shiga tsakiyar gidan, sai na hango Mal. Bala ya zage yana ta dukan '_Yar sa sabuwa har da yayyanta maza guda biyu Danbaba da Sule,
a gefe guda kuma mahaifiyar ta da sauran yan gidan musamman yan'uwanta suna ta kuka, cikin karfin hali na yi kokarin kwatar Sabuwa daga hannun mahaifinta, sai mahaifiyarta ta riko ni cikin kuka tana fadin ki bar shi ya kasheta tsinanniya ta janyo mana abin kunya ciki ta yo.
.
Na cika da matukar mamaki na yi kokarin ganin na nusar da wannan iyayan ba ta haka ya kamata su hukunta sabuwa ba, amman suka ki saurarata har na fusata na yi kokarin ficewa, ganin hakan ya sanya mahaifin ya sauko domin ya na ganin ina cikin jarin mutanan da na ke ba shi taimako a duk lokacin da suka shiga wata matsala musamman idan ya tafi fataucinsa ya yi wata biyu zuwa uku bai dawo ba.
Cikin kokarin yin kuka yake min bayanin shi da sabuwa har abada kuma ba don ni ba da wallahi sai sun kasheta sun kashe banza, daga nan ya fice a fusace.
Ni na kama Sabuwa wacce ko ina a jikinta ya fashe na fara rarrashinta tana kuka tana fadin wallahi Anty tsautsayi ne, na yi kokarin rokon mahaifiyar ta akan ta taimaka mata da ruwan dumi sai ta ce Allah ya kiyaye ta kara taba tsinanniya.
.
Haka kowa ya bar mu da Sabuwa na shiga gidana na kawo mata ruwa ta yi wanka da abinci ta ci da magani.
Sannan na fara tambayarta garin yaya hakan ya faru, me ya sa..?
Cikin kuka tace min Anty babu wanda ya min wannan tambayar tun da aka gano wannan matsalar sai ke, yanzu ina jin zazzabi amma gobe zan miki bayani, sai dai ki sani Anty da zaa sami iyaye irin ki da al'umma sun rage matsaloli nagode Anty.
.
Haka na dawo gida cike da damuwar abin da ya sami Sabuwa domin na san yarinya ce me kokarin kare kanta da mutuncinta, sannan ina ji a raina idan wani nawa yayi laifi makamancin abin da Sabuwa ta yi ba haka zan mata hukunci ba.
.
Washegari da safe ina shirin shiga domin na ji yanda Sabuwa ta kwana sai na kara jiyo hayaniya a gidan da koke-koke da gaggawa na zagaya.
Sai na tarar da yan gidan tsaye carko-carko wasu na kuka, jin Mal. Bala yana fadin 'Tafi ruwa gudu, Allah ya raba ni da masifa.'
Na fahimci Sabuwa ta gudu ne.
.
Abu daya ya tsaya min a raina shine bayanin da Sabuwa ta ce za ta yi min. Tun daga wannan ranar kullum sai na yi tunanin ina Sabuwa ta ke.
Shin a matsayinka na Uba ko Uwa ko dan'uwa ko yar'uwa me ya kamata ki yiwa wani na ki da ya shiga matsala, har yanzu wasu daga cikin hausawa sun kasa gane yanda ake tarbiyyar wanda ya fandare sai tsinuwa da la'anta da kyama....?

___Copied Real Fauziyya D Sulaiman
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts