NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

SHIN KO KINSAN ILLAR ABORTION AGAREKI?????

RKO KINSAN ILLAR DA ABORTION KE YIWA JIKIN KI, (ZUBAR DA CIKI)

bayaga haramcin dake tattare ga kisan mutum da zubar mutunci a idon jama'ah , akwai illoli dadama da zubarda ciki ke yiwa macce ga lafiyar ta ...

😔duk sanda ciki yakai wata 3 zuwa 4 yafara girma babu kwayoyin maganin da zasu zubar dashi sai anbude bakin mahaifa da karfi a ciro mutum ,

-kisani daga wannan lokacin bakin mahaifar yasami matsala dan anbude shi ba a lokacin da yadace abude shi bane,

- zaki sami zubar jini mai muni idan baayi nasara ba har takai ga bugawar zuciya

-kananan cututtuka sun zama costomers ga mahaifar ki, kullun sai kinsha maganin wannan ciwon gobe na wannan ciwon daganan har sukai ga zama P.I.D

- zaki sha wahala kandin sinadaran dake daidaita haihuwa da rowan nono su daidaita ajikin ki,

-idan baayi nasara ba kowacce haihuwa zata zo da matsaloli saboda samuwar matsalar mahaifa

😔Idan kuma na kwayoyin magani akayi,,
-ciwon baya mai tsanani

-zazzabi maras misali

-jiri da amai da ciwon ciki

-wadansu magungunan kashe mahaifa suke gabadaya, kuma su tsayar da haihuwa ga macce

-wasu kuma sukan bude kuma su lalata bakin mahaifa har ma wani lokaci ko macce tayi aure da zarar tasamu ciki sai ya zube saboda an lalata bakin mahaifar

-kamar yanda kuka sani shan wasu magunguna nada hadari, to saboda hadarin wasu ne kesa su zubar da ciki amma babu kwayar da akayi kacokan saboda zubar da ciki, saidai illar maganin ta zubar da ciki, shine wasu matan ke siya suna amfani dashi

SHAWARA,,
idan bakida aure kuma bakison haihuwa, to kiyi amfani da magungunan family planning yafi sauki ko amfani da condom akan sai kinsami ciki ki zubar dashi, watarana zaki rasa rayuwar ki,

Mai ciki da mai zubar da ciki su tuna hukuncin kisan mutum, babu addinin daya halatta zubar da ciki,

Akarshe,, atsaya akan iyakokin Allah dan kaucewa matsalolin lafiya da kuma tsira da mutunci ga mutane da kuma tsira gobe kiyama,,,

Allah ya karemu da son zuciya yasa mufi karfin zukatanmu..

#VANGUARD
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts