NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

SHAWARA GA MASU JINNU (Aljanu )


πŸ‘» *ALJANI NE A JIKINKI //4* πŸ‘»

*SHAWARWARI GA MASU JINNU*

Duk wanda yake fuskantar matsalolin na jinnu akwai abubuwan da ya kamata ya fahimta kuma ya kiyaye.

πŸ‘»1. Mafiya yawan mutane basa ganin tasirin magani ne saboda a zuciyar su suna kokwanto, duk kuma abin da kake kokwantonsa to abu mai wuya ne ka ga tasirin sa. Idan Annabi yace wannan addu'ar zata kare mutum daga dukkan wani abun cutar wa daga safe zuwa yamma, ko daga dare zuwa wayewar gari to kiyi Imani 100% cewa Allah zai baki kariya. Annabi shine mai gaskiya abin gasgatawa da yace Habbatus sauda tana maganin dukkan cuta ban da mutuwa to sai kiyi imani cewa idan ina amfani da ita zaki warke daga dukkan cuta. Sai ki ga cikin yardan Allah kin nemi matsalarki wata rana ki ga bashi.

πŸ‘»2. Hakuri da gujewa gaggawa, idan an baki addu'a ko magani kada ki ďauka yanzu yanzu ko gobe ne zaki warke a'a, kiyi ta addu'a kina magani a kwana a tashi zaki nemi matsalarki ki rasa, domin Allah yana amsa addu'a mutuqar bawa bayyi gaggawa ba. Zaka ga mace tayi shekara tana abu, ta samu saukin wasu abun amma bata warke duka ba sai ta ce ita ta gaji da wahala wannan maganin baya mata komai sai ta dai na.

πŸ‘»3. Kiyayewa dukkan abin da akace ki kiyaye da aikata dukkan abun da aka ce ki aikata da kuma jajircewa, kada ki fara amfani da magani ko ki fara yin addu'a kiji sauki bayan kwana biyu ki watsar da komai ki koma rayuwar ki ta da, idan baki wasa ba in ya tashi dawo miki sai yayi har da gayya, domin aljani in shi kadai ya shige ki in yaji dadin wuri sai yayi ta miki gayyan wasu.

πŸ‘»4. Kiyaye neman magani ta hanyar zuwa wurin malamin duba ko boka, hakika haramun ne wannan, kada kije wurin wani mai aiki da aljanu kice ya rabaki da naki, in bai rabaki ba ya qara miki wasu. Kuma abun da zasu yi shine wai sulhu, aljani ya fadi me za'a masa sai a masa ya bar jikinki. Zai iya yi kamar ya tafi, in aure ya hanaki to zaki ga kin samu kin yi amma yana nan bai tafi ba, iyaka ya dai na azabtar dake ne saboda ki aminta da boka da kuma aikinsa, kin gane hikimar da suka yi amfani da ita? Ana nan kuma wata rana komai zai dawo sabo, sai ki sake rugawa wurin boka sai yace ai wannan asiri aka miki ba waccen matsalar bace, a haka zasu yi ta dulmiyar dake. Boka ba zai iya baki tsari ba Allah ne mai tsarewa, asaran kudin ki kawai kike yi kina sake jawo ma kanki masifa. Don haka shine your eyes sister.

πŸ‘»5. Abu na gaba shine yaqi da zuciyar ki, 'yar'uwa suna yaqin kine kema kina yaqar su da ayoyi, addu'oi da ingatattun magungunan Manzon Allah. Kada idan suna nuna basa so ki biye ki dai na, a'a kiyi yaqi, idan kin yi amfani da wannan kin sha baqar wuya gobe ma haka zaki sake yi ba fashi. A haka haka tun kina yi kina shan wuya har wata rana zaki wayi gari baki jin komai har kiyi ki gama.

πŸ‘»6. Kokarin tsananta addu'a da roqo. Idan an miki ruqya aljani zai iya ya gama ihunsa ya jigata ya gudu, wani dan gatan ma ana kawo ki gaban mai ruqya zai fice, ayi karatun a gama duk bashi ma abin sa, bayan kun gama kuma sai ya dawo, haka nan in magani ne, zayyi nesa dake ya qi shigowa jikinki ko ya fita a jikinki in mazauni jikinki ne, saboda maganinki na azabtar dashi, to amma yana nan yana jiran randa zaki dai na, sai ki ga komai ya dawo miki sabo, sai kuma a sake komawa wurin mai ruqya? Amma in kece kullum kike addu'an ki babu fashi fa? Har abada shi dake, saboda ba zai taba samun daman shigowa ba don kullum cikin kariyan Allah kike. Ki zama mai ruqyan kanki.

πŸ‘»7. Shawarar qarshe itace koyon adduoi, musamman na safiya da maraice, babban sakaci ne ace babu wasu addu'oi da kika iya a kanki wanda ko baki duba littafi ba zaki karanta don neman kariya ba, duk addu'ar da aka baki aka ce na kariya ne daga shaidanu haddace shi ya kamata kiyi. Duk lokacin da kika ji alamar aljani zai shigo jikinki ko kika ji wani iri fara addu'oi kada ki dai na har sai kin dai na ji. Ba wai kawai ki zauna komai sai kin duba paper ba yanda in baki tare da paper shikenan zaki zauna ba addu'a saboda baki iya ko daya ba.

Ina roqon Allah ya kare mu daga sharrin aljanu da shaidanu.

Rubutawa:- Sadiya Lawwal Abubakar
Gabatarwa:- YUSHAU A. BAWA

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren πŸ”‘ *_DAARUL HAQH_* πŸ”‘ (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren DAARUL HAQH a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (08030746582) ta ‎whatsApp.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts