NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

MENENE MUHIMMANCIN MOTSA JIKI?????


MENENE MAHIMMANCIN MOTSA JIKI? Wanne lokaci Ya dace
Ayi?
-@-------------------@
Ba shakka motsa jiki akai-akai na daya daga cikin hanyoyin
samun koshin lafiya. Bincike daban-daban ya nuna cewa
motsa jiki kan hana cututtuka irin na zuciya da na mutuwar
barin jiki aukuwa, ta hanyar kona man cholesterol, da rage
hawan jini, da rage siga a jiki ga masu ciwon siga da ma
wadanda basu da ciwon.
Wato dai a hannu daya motsa jiki riga-kafi ne babba daga
ciwon siga, ciwon zuciya, kiba, ciwon hawan jini, ciwon
mutuwar barin jiki, wasu ciwukan na daji wato kansa, ciwon
baya, ciwon jiki, ciwon damuwa na depression, ko na kasala
da ma wasu da dama.
A daya hannun kuma motsa jiki kan yi maganin duk wadannan
ciwuka idan basu yi nisa sosai ba, Bincike kuma yaci gaba da
nuna cewa mai motsa jiki akai-akai bayan annashuwa da zai
rika ji a ransa, da kuma jin karfin jiki ta hanyar kara kwarin
kashi ana sa ran kuma zai samu tsawon shekaru da kwarinsa a
duniya.
A mafi yawan lokuta mutane sun fi jin dadin motsa jiki da safe
domin lokacin hakan zai warming din jijiyoyi ya habbaka blood
circulation da kuma saurin narkewar abinci ajika, amma
masana sun tabbatar da cewa ko da wane lokaci ma ana iya yi
don za a iya samun duk fa’idojin da ake samu da safen.
Sannan ba wai kawai mutum ya zage da tikar gudu a fili shine
kawai motsa jiki ba, a’a idan ka yi tafiyar minti 45 a kowacce
rana ko da mintina 15 sau uku (wato ya dai tashi minti 45)
indai za ka yi a kullum, to kana daya daga cikin mutane masu
motsa jiki sauran ko adaki ayi kamar yadda hoto ya nuna.

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts