NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

MATSALAR JININN HAILA DA CIWON MARA NA MATA.......

MATSALAR AL'ADA DA CIWON MARA GA MATA.
Kamar yadda mukasani, mata kan fiskanci matasaloli daban daban yayi zuwan alada ta xubar jini kokuma wani farin ruwa daban.
Ciwon mara a yayin alada kan farune yayin da mahaifa ke curewa da motsawa waje guda domin fitar da wani abu daga cikinta marar amfani wanda wannan motsin shike saka ciwon mara.
A lura cewa akwai ire iren abubuwa dakan zuba daga alaurar mata kamar jini ko mai hade da ruwa ruwa, farin ruwa, ruwa mai kauri, ruwa mai wata kala daban, d.s wanda hakan kan farune sbd wata matsala ta shigar kwayoyin cuta, kodai ta virus, yeast infection, shan kwayoyin hana daukar ciki, saduwa barkatai, ciwon suga, cancer, shan barasa d.s. Idan anga haka sai a gaggauta xuwa ga likita. Wani lokaci alada kan rikice ko tsallake bakuma tare da shigar cikiba.
Zubar jinin haila ko wankin kamara yadda ake fada, kowace mace nada nata mataki daban daban wanda kan auku musu kafin saukar jinin a kowane wata. Wannan jini kan sauko ne daga mahaifa wanda kuma daxarar ya dauke anfi daukar ciki musammam kwamaki hudu ko biyar na farko. Zaifi kyau a lura da xuwan lokacin alada da adadin yawan jinin da yawan kwanakin daya dace wadda idan har yayi nisa shine kwana shida amma ga yan mata yara baya wuce kwana daya xuwa biyu.
Idan ana fama da ciwo yayin alada ko lokacin karatowar alada, ko fama da ciwon mara, ciki, rashin walwala, kin cin abinci, kasala, nauyin jiki, tashin zuciya d.s. To a lura cewa, akwai matakai daya kamata abi don samun sassauci kamar:
1. Sanin alamomin xuwan jinin kafin ya sauka, hakan kan temaka wajen tsara alamuran yau da kullum da ragewa kai wahala dakuma samun nishadi, motsa jiki dacin abu marar nauyi.
2. Lura da abubuwan da ake ci lokacin alada ko karatowarta, da rage cin gishiri don yana tara ruwa yakuma hanashi fita idan yayi yawa sai jiki yafara nauyi da kumburi. A kuma guji cin soyayyun abubuwa da gyada, yaji, kayan filawa, naskofi, lemon kwalba, goro, koko, barasa (giya) d.s. Don suna rikita lokacin alada. A rika yawaita cin 'ya'yan itatuwa, shayi mai kyau don suna rage ciwon na mara.
3. A rage shan magunguna barkatai.
4. Xaa iya amafani da magugunan karin jini idan haila ta yawaita.
5. Idan mara ko ciki na ciwo sosai, zaa iya kwantawa waje daya ta hanyar jingino da matashi dakuma yin numfashi kamar ana hakki.
6. Akan kuma iya bada nauyi ta kasa da doka gadon baya ko shafa kan mara idan harta kulle da ciwo. Haka kuma idan ciwon yayi tsanani da yawa, akan iya jika tawul da ruwan xafi ko sanyi a dora a saman mara ko goshi, hakan kan kawo sassaucin ciwon. A lura da tsafta da kayan amfani na yau da kullum kamar abinci, sabulu, man shafawa d.s. Abubuwa da dama kan faru, amma mafi kyautatuwa shine zuwa asibiti. Allah yasa mu dace DAGA LAFIYA JARI

MOM AISHAYea
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts