NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

LET'S TALK ABOUT MAKEUP ....... YANDA AKE MAKEUP

LET'S TALK ABOUT MAKEUP 💁

EPISODE : 10
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Last week mun fara magana akan concealer yanda zaki saya da kuma wanda zai dace dake So, insha Allah Yau zan gabatar maku da hanyoyi daban daban wanda zaki iya amfani da concealer dinki amma kafin nan akwai buqatar in qara tunasar da mu wannan

YELLOW CONCEALER :- tana fitar maki da even tone ma'ana zata sa kalar fatar ki ta fito sosai

PINK AND PEACH CONCEALER
Wannan kalar sun fi kyau a shafa su a under eye wato ina nufin concealer da ake shafawa a qasan ido

GREEN CONCEALER
wannan kalolin concealer din suna boye blemishes wasu en chaki chaki pimples, tabo da duk wasu dabbare dabbaren da suke a fuskar mutum

ORANGE CONCEALER
Wannan especially mata masu amfani da niqaf zaki ga zagayen idon su tayi baqi sabda rana tou idan idonki yana da wannan duhun akwai buqatar ki yi amfani da orange concealer a idon ki

PURPLE CONCEALER
swannan yana boye chaki chakin fuska

Wannan sune kaloli na concealer da ya kamata ki mallaka alhmdl ynxn zaki iya samun su cikin arha da sauki domin anyi su kamar eye shadow idan kin je siya kawai kice a baki CONCEALER PLATELET .

YANDA AKE AMFANI DA CONCEALER
Concealer tana da amfani a. Wurare iri daban daban misali

1 MACE MARAR TABO
Ba dole sai kina da tabo a jiki zakiyi using concealer ba a'a zaki iya amfani dashi wurin fitar da asali shape din fuskar da Allah yayi maki yanda zakiyi shine ki samu concealer kala biyu mai haske da mai duhu (kamar yanda nayi Bayani a post dina na last week idan baki gani ba ki duba a Facebook page mai suna ADO DA KWALLIYA ) ki shafa mai hasken a T zone dinki da kumatun Ki mai duhun kuma ki shafa a sauran sassan fuskar ki zuwa wuya sannan kiyi Blending ki shafa powder.

2 MACE MAI TABO KO PIMPLES
ke kika fi chanchanta wurin amfani da concealer sai ki sayi concealer na boye tabo ki shafa a kan tabon kadai a duk fuskar ki ba fa! ki bari ya dan sha iska kamar 5mins sannan sai ki dauko asalin concealer din ki kalar skin naki ki shafa akan green concealer din sannan ki shafa powder.
Idan baki da concealer zaki iya amfani da foundation amma idan ki shafa sai kin jira 30mins ya yi kauri sannan ki shafa powder akai

PIMPLES A BAYA KO QIRJI
idan kina da pimples ko tabbai da yawa ko kadan a jikin ki kuma kina sou ki sa kayan da dole sai sun fito.....
Ki dauki normal concealer dinki kalar jikin ki sak! Ki shafa a wurin amma fa tabon da pimples din kadai zaki riqa rufe wa ba wai duk wajen zaki yiwa fenti ba. Idan kin gama sai ki yi amfani da brush ko soson pauda ki shafa pouda mai gari a wajen sama sama ake shafawa ba da qarfi ba .

MARAR SON KWALLIYA / STUDENTS
Man shafawar ki ta fuska zaki dangwali kadan ki shafa a bayan hannun ki hada da concealer da foundation ki kwaba ki shafa a fuskar ki at once ki shafa powder amma fa kadan kadan kar ki cika idan kikayi haka kin hada TINTED MOISTURIZER kenan amma baza ki iya hadawa da yawa ki ajiye ba.

CONCEALER A QASAN IDO
- Hanya Mafi dacewa idan zaki shafa concealer a kasan idon ki shine kiyi shape din triangle dashi kamar yanda zaku gani a hoton .
- Sannan kar ki manta idan idonki yana da duhu tou ki riqa amfani da orange, pink ko kuma peach colour concealer a qasan idon sannan sai ki rufe shi sama sama da asalin concealer dinki.
- akwai wasu layi layi a qasan idon ki idan kin gama shafa concealer kinga sun fito sai ki nema tissue ki rage wa tissue din kauri wajen cire palle daya a jiki ki sa a qasan idonki zai tsantsame maiko din.

CONCEALER A GIRA
-zakiyi amfani da concealer brush wurin fitar da shape din girar ki ta sama da ta qasa sannan kiyi amfani da yatsar ki ta zobe ki rage wa concealer din karfi sosai kar ki bari ta fito dau

CONCEALER A IDO
- idan baki da eyeshadow primer zaki iya amfani da concealer wato zaki dangwali concealer dan kadan sai ki shafa a saman idonki amma fa kar bari ya shiga ramin kashin idonki tou bayan kin shafa sai ko shafa farin eyeshadow akai sannan ki shafa duk kalar da kike sou hakan zai sa eyeshadow din yayi kauri kuma ya tsaya a wuri daya ba tare da wani layi layi ba.
-idan kina shafa eyeliner a ido kika yi mistake kar ki damu idan kin gama ki sa abun share kunne ki goge inda aka samu matsalar na San bazai fita duka ba sai ki shafa concealer a wurin.
-ki fitar da shape din idonki ta hanyar shafa concealer a saman kwayan idonki sannan ki tsallake ramin qashin idanki ki shafa a qashin girar da saqon idonki da ta qasan amma fa ba yanda za'a gane ba yin hakan na da kyau musamman lokacin da kika tashi daga barci idonki luhu luhu.

CONCEALER A BAKI
-idan zaki shafa jambaki mai kala biyu bakya sou su gauraya su zama daya zua anjima toh ki shafa concealer a zagayen bakin naki inda zaki amma banda tsakiya sai ki dan yi blending dinsa.
-idan kuma kina sou bakin ki yayi kauri kamar mai shirin yin kiss tou zaki yi amfani da concealer wurin fitar da shape din kiss a tsakiyar bakin ki sai kiyi Blending sannan ki shafa jambaki a hankali
-amma idan kina sou ki fitar da shape din bakin ki ne tou wannan zaki shafa concealer a gaba daya labban ki sannan ki shafa jambaki idan kin gama sai kiyi amfani da concealer brush wurin qara fitar da shape din bakin naki ta inda jambaki ya bata.

CONCEALER A QASHIN WUYA
yanda zaki fitar da sexy night time look da qashin wuyan ki shine ki samu concealer kala biyu mai haske da mai duhu sai ki daga kafadun ki sama ki shafa mai duhun a aljuhun da sukayi mai hasken kuma a qashin saman sai kiyi Blending dinsu yanda ba za'a gani ba.

Wannan sune da yawa daga cikin abubuwan da nasan anayi da concealer don haka nike ganin Gaskia ya kamata ki mallaki concealer kala kala iri iri daban daban amma dai ki tabbatar kin fara shafa foundation kafin concealer ba wai shafa concealer a kasan foundation bashi da kyau bane a'a sai dai yana buqatar kwarewa. dan Allah duk wacce ta ji dadin abun da na rubta ta taya ni addu'a bukatun mu na alkhairi Allah ya biya mana Amin
Wslm

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts