NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

KARANCIN BACCIKARANCIN BACCI [SLEEPING DEPRIVATION]
Wannan wata babbar dabi'a ce dana kuma tsinkayowa shine
yadda muke shagala gami da hana kwakwalwar mu hutu.
Karancin bacci na kirashi da Sleep deprivation ne Saboda ya
bambanta da Rashin bacci wato (insomnia) a kimiyyance.
Karancin bacci mutum shike tursasa kansa kin yin bacci wanda
kuma akansa ne zan magana, Yayin da rashin bacci mutum shi
yanason Yi Amma ya kasa watakil Saboda wata larura dake
damunsa irinsu hawan jini, Ciwon TB, da sauransu.
Mun shigo wani yanayi da mutane da yawa sun baiwa
abubuwan more rayuwa mahimmanci da lokacinsu yayin da
kwakwalensu ke son hutu. Misali yadda social media ta zo ma
mutum da yanayin da shi kadai adaki sai yai nishadi da
wayarsa batare da bukatar abokin HIRA kusa dashi ko kusa da
ita ba wanda kuma hakan nasa matsi gami da illa ga lafiyar
mu.
Samun isashshen bacci abune dake ha66aka lfy shyasa
wannan lokutan cuttuka su kaima matasan mu mata da maza
yawa. A duniya ayanxu kaso arba'in 40% na mutane na
fuskantar wannan larura, Shiyasa cibiyar lfy ta CDC ta Kira abun
da annoba wato (sleep deprivation epidemic era). Gsky yana
da kyau muba bacci mahimmanci ba daidai ne ma mutum
yakai karfe 11 na dare bai kwanta ba matukar ba isashshen
baccin rana ya samu ba.
YA YA KAMATA BACCIN YA KASANCE
Wannan shine adadin awoyin da ya kamata kowa ya samu
yayin bacci.
1 Sabuwar haihuwa (Newborn) daga ranar haihuwa zuwa
watanni 3 aduniya na bukatar baccin awoyi 14-to-17hours
kullum.
2 Jariri (infant) dan watanni 4 zuwa 11 na bukatar baccin
12 to 15hours kullum.
3 Yaro (toddler) dan shekara 1----2yrs na bukatar baccin
awoyi 11 xuwa 14hours kullum.
4 Dan nursery (pre school age) wato dan 3----5years na
bukatar baccin awoyi 10 xuwa 13 kullum.
5 Dan makaranta (school age) wato 6----13 years Shima na
bukatar baccin awoyi 10 to 13 years.
6 Matashi (teenager) dan 14 to 17years yana bukatar baccin
awoyi 8 Zuwa 10 kullum.
7 Samari (young adult) dan 18 to 25years na bukatar baccin
awoyi 7 zuwa 9hours kullum.
8 Manya (Adults) daga shekara 26 zuwa 64years na bukatar
baccin awoyi 7 zuwa 9hours a kullum.
9 Dattawa (Older Age) daga shekaru 65+ zuwa sama na
bukatar baccin awoyi 7 zuwa 8 kullum.
ILLOLIN KARANCIN BACCI
A Yana jawo taruwar nauyi ajika (weight gain).
B Yana raunana garkuwar jiki.
C Yana kawo hawan jini.
D Yawan mantuwa
E Toshewa tare da fashewar Jijiyar jinin kwakwalwa
(stroke).
F Ciwon zuciya.
G Hatsarin kamuwa da Ciwon suga rukuni na 2.
H Sauyin dabi'u.
I Da sauran matsalolin jiki da ba'a zato.
SHAWARA
Lallai mu duba adadin awoyin baccin da muke yi matukar
mukaga ko kusa da wadannan awoyin bama Yi to lallai wajibi
ne mutum ya gyara domin hausawa na cewa wai kowa lfy
taima dadi barin mai itane.
Allah yasa munji mun kuma fadak
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts