NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

KALOLIN BREAKFAST 🍳 (Types of breakfast 🍳)


Breakfast
Akwai kalolin abinci da dama da uwargida xata iya yima oga Shi amatsayin breakfast.ba sai kullum tea kadai bah.
Kalolin abincin sun hada da
1.uwargida xata iya surfa wakenta tayi ma oga kunu da komai
2.xaki iya fryin yam nd egg saiki dama masa custard.
3.xaki iya yi masa chips da er sauce ta tarugu sai ki fryin egg aci da quaker oath.
4.sai kuma in kina iyawa da daddare kin dafa kan ragon ki yayi romo mai dadi da safe ki dumama sai kiyi maasa aci da Roman.
5.idan ya siyo bread kina iya soyawa da kwai suyar tay kyau kar yasha Mai sai aci da custard.
6. Kina iya yin yamballs aci da koko.

AMALA
Garin doya kofi 1
Ruwan zafi kofi 2
Kanwa
Idan kika tafasa ruwa sai ki dinga barbada garin doyar a cikin ruwan kina tukawa da muciya don kada ya yi gudaji, sannan ki kara ruwa zafi ki tuke shi ya tuku sosai amman kada ya yi tauri a ci gaba da tukawa har sai ya chanja kala ana ci da miyar ganye ko miyar yauki.


SULTAN CHIP

Dankali 6
Albasa 2
Tumatur 2
Attarugu 2
Maggi 2
Tafarnuwa 1
Curry

A yanka dankali a soya sama sama, a dafa nama da albasa daya da kayan kanshi idan ya dahu a ajiye ruwan naman gefe daya, a nika naman. A yanka albasa, attarugu, tumatur da tafarnuwa.
A dora ruwan naman a kan wuta, a zuba nikakken naman da yakkakun kayan miya tare da soyayyen dankali, maggi,gishiri da curry yanda zasu isa. A bari su dahu minti 10-15 har sai ruwan ya tsotse.


POTATO CAKE

Dankali 6
Kwai 5
Koren tattasai 1
Albasa
Mai
Maggi
Gishiri
Kayan kanshi

A yanka danyen dankali kanana kamar dunkulen maggi ko kasa da haka. A yanka koren tattasai da albasa, a soya sama sama, a hada su da dankalin tare da maggi, gishiri da kayan kanshi.
A zuba mai kadan a kwanon suya (fryin pan) idan yayi zafi kadan a zuba dakalin.
A fasa kwai a kada a zuba a kan dankalin, a kuma tabbatar kwan ya rufe dankalin, a bari har sai dankalin ya dahu sannan a sauke a yan yanka shi kamar cake dai dai girman da ake bukata.


KUSKUS MAI KWAI DA NAMA

Kuskus
Nama
Kwai
Albasa
Maggi,gishiri, curry
Attarugu
Mai
Za ki dora ruwan zafi kofi hudu sannan ki bude kus kus leda daya ki juye a kwano idan ruwan ya tafasa sai ki juye a kan wannan kus kus din ki rufe, sannan sai ki yanka nama dogo dogo sirara kamar tana ki dafa shi sanna sai ki yiwa albasa attarugu da koren tattasai irin yankan da kika yiwa naman sai ki zuba su da dan mai ki soya ki ajiye, sannan sai ki fasa kwai shi ma ki yi masa suyar burus burs, sannan ki zuba mai kadan ki zuba kus kus din kina soyawa har sai kin ga ya yi wara wara sai ki kwashe shikenan aci lfyπŸ˜‹πŸ˜‹ROMON NIKAKKIYAR KAZA

Kaza
Kwai
Rwan dahuwar kaza
Waken gwan gwani
Dankali 3
Albasa
Maggi gishiri kori
Attarugu

Da farko zaki tafasa naman kazar ki da kayan kamshi ida yaya saki soya sama sama ki nike ta ki zuba a kwano, sai ki hada shi da kwai attarugu, maggi, gidhiri da kori ki chakuda su sannan ki lulaya su kamar ball
sannan ki samu ruran kaza dankali da albasarki ki dafa su daban har sai dankalin ya dahu amma shi za ki yanka shi kamargidan suga bayan sun dahu sai ki kawo kwallon namanki da waken gwangwanin ki zuba a kai ki bar shi ya dahu zuwa kamar mintuna, sai ki kankare karas ki yanka shi falan falan ki zuba a kai ki barshi sai ya dahu shikenan.COCONUT WAFERS

KAYAN HADI

*Kwakwa 1
*Bota 1/2 gwangwani
*Sikari 1.2 kofi
*Filawa kofi 1
*Lemun tsami 1/2 chokali
*Zuma rabin chokali

YADDA AKE HADAWA

A kwaba sikari da botar har sai sunyi lukub lukub, a zuba zuma a matsa lemun tsami, a gurza kwakwa a zuba sannan a zuba filawa a chakuda.
A rika zuba hadin da chokali akan farantin gashi amman kada asa su a kusa saboda kada su game. A gasa a obin kamar minti goma sha biyu, a bari ya huce kafin a cire daga kan farantin gashin.

ROMON TSOKAR KAZA

Kaza
Albasa
Attarugu
Mai
Gishiri, maggi, kori
Kayan kamshi,tafar nuwa

Da farko za ki cire fatar kazar sannan ki yayyanka ta siri siri da wuka mai kaifi sai ki zuba ta a kaskon da albasa atatarugu,gishiri,maggkori,kayan kamsahi, tafarnuwa da mai sannan ki rufe ki dora a kan wuta, su dan tururu na yan mitina kina dubawa, har ya yi kauri sai ki sauke aci lfyπŸ˜‹πŸ˜‹πŸ˜‹

COCONUT BISCUTTS

*Kwakwa 1
*Filawa kofi 1
*Rogo rabi
*Sikari kofi 1
*Madara kofi 1
Kwai 2
*Bota 1
*Lemun tsami 1
*Lemun zaki 2

YADDA AKE HADAWA

A yanka a fere a gurza kwakwa da rogo, a zuba madara, da ruwa a matsa lemun tsami da lemun zaki a chakuda sosai sannan a zuba kwai, a chakuda har sai filawar ta hadu sannan a mirza a yanka su yadda ake bukata a gasa a obin.COCINUT KISSES

Kwakwa 2
Kwai 4
Sikari kofi 1
Gishiri

A fasa kwai a cire dorawan (kwanduwa) a zuba gishiri a farin kwan a kada sosai, a zuba sikari a ci gaba da kadawa har sai ya narke. A gurza kwakwa a zuba a ciki.
A rika zubawa da chokalin shan shayi (teaspoon) akan farantin gashi a gasa a ibin kamar minti ashirin.


CHOCILATE PUDGE

Sikari
Madara condensed 1
chakulet 1
Ruwa

A dora ruwa da sikari a kan wuta har sai ya narke sai a zuba madara (condensed milk) a rika juyawa saboda kada tayi kamu a cire a cire daga kan wuta, bayan minti biyu a zuba cakulet (wanda aka gurza)
A kada su har sai yayi kauri sosai. A shafa butter a gwangwanin gashi (baking tin) a zuba hadin madarar a ciki, a saka a firjin ya samu kamar awa biyar sai a fiddo a yanyanka.


EGG CUSTARD

Kwai 4
Madara gwangwani 1
Sikari chokali 2
Flavour 1/4 chokali

A kada kwai, a kara madara da sikari. flavour da ruwa kadan a juya sosai sannan a kulla a leda a turara a cikin ruwan zafi ko kuma a gasa da obin minti talatin. A barshi ya huce ko kuma a saka a firjin idan ana bukatar hakan.

EGG INTO EGG

Kwai 5
Albasa 1
Attarugu 1
Tumatur 1
Maggi
Gishiri Busasshen Biredi
Curry
Mai

A dafa kwai hudu, a yanka tumatur, attarugu da albasa a soya sama sama a zuba maggi da gushiri, a bare kwan a yanka saman a hankali a cire dorawan kwai a hada da garin biredi da su attargu da albasar, a chakuda.
A dundunkule hadin albasar a saka cikin farin kwan a mai da murfin a rufe, a kada kwai da garin biredi a dinga tsoma da[truncated by WhatsApp]
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts