NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

HANYOYIN DAZAKI BI KIMAIDA MIJINKI MIJINTACE

R

*👩🏻 KI GYARA DA KANKI👩🏻*


*Lakanoni 52 na iya mayar da mai gidanki mijin Tace*

Wadananan shawarwari ne wadanda Idan mata Suka yi la'akari dasu in sha Allah za'a samu kyautata wajen zaman aure.
Muna addua Allah ya bada ikon kiyayewa.

1- *Aurenki ya zama domin neman yardar Allah kika yi badan Tara abin duniya ba*

2- *Kada ki zama mai kwadayi wajen zakin mijin aure*

3- *Ki zabawa 'ya'yanki uba ta hanyar auren Wanda kika yarda da addininsa da dabi'unsa har ma da dangantakarsa*

4- *Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki*

5- *Kada Ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki*

6- *Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki*

7- *Ki zama mai mutukar biyayya ga mijinki*

8- *Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala*

9- *Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya*

10- *Kada Ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki*

11- *Kada Ki zama mai rainuwa acikin duk abinda mijinki ya baki*

12- *Ki dunga godewa mijinki acikin abinda ya baki*

13- *Ki dunga wanke bakinki musamman lokacin kwanciya bacci, kuma ya zama Abu na farko bayan tashi daga bacci*

14- *Ki zama mai Tsaftar jiki, gidanki, abincinki, wajen kwanciya bacci da sauransu*

15- *Girmama iyayen miji, 'yan uwansa da abokansa yana da mahimmanci sosai*

16- *Kada Ki zama mai satar kayan mijinki*

17- *Ki guje leke lokacin da maigidanki baya nan Dan yana ruguza aure musamman cikin hausawa*

18- *Ki kiyaye abinda mijinki yafi so*

19- *Ki gane abinda mijinki yafi son ci da safe, rana da kuma dare*

20- *Ki dunga yabon kwalliyar mijinki*

21- *Ki dunga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi*

22- *Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar Oga*

23- *Ki zama mai sanya turaren wuta a dakinki kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki*

24- *Lallai Kiyi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki*

*Zan tsaya a nan sai mun hadu a rubutun na gaba*

*_Ki kokarin tura yan uwanku mata Dan su amfana_*

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts