NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

HANYOYI 25 NASARRFA DANKALIN TURAWA DANA HAUSA

*🥔HANYOYI 25 NA SARRAFA DANKALIN TURAWA DA NA HAUSA 🥔*

Tambayoyin yan uwa mata sun yi yawa a kan yadda za su sarrafa dankali ba kullum a soya shi a ci ba. Hakan yasa na tattara muku hanyoyin da za a yi amfani da su.

1- *In breakfast (A abincin safe)*


1-Cheese and potatoe pie: A zuba tafasasshen ruwa a kan instant potatoe ko a dafa dankalin turawa ai mashing din sa (a daddaka) a saka butter da gurzajjen cheese(cukwui) a ciki sai a zuba shi a mazubi me dan zurfi sai a sa a oven. In ya fara gasuwa sai a fito da shi a zuba ragowar cukwin a kai a mai da shi sai cheese din ya narke sai a fito da shi. A yi masa ado da yankakken tumatir.

2- A gurza danyen dankali a dan barshi a ruwan ya jika kadan sai a daka nama a hada da dankalin a sa attaruhu,albasa,dandano sai a fasa kwai a juya. Sai a dinga diba ana soya shi a mai.

3- Wainar kwai da dankali: A yanka dankali cubes sai a dafa ko a soya shi sai a kada kwai a sa albasa da dandano. Sai a zuba dankalin a cikin kwan a soya shi kamar wainar kwai.

4- Doughnut : A dafa dankalin turawa a daddaka shi a zuba a kwabin doughnut yana dadi sosai.

5- Potatoe Sandwich: A gurza dankalin turawa da carrots sai a zuba mai kadan a kasko da albasa a soya kadan sai a zuba dankalin ai ta juyawa a zuba carrots da dandano da kayan kamshi, in suka yi laushi a sauke. Sai a dauki bread slice daya a shafa hadin a kai a rufe da wani slice bread din. In ana so za a hada da dakakken nama a wajen soyawar. A ci haka ko da tea.

6- Sultan chips: A yanka dankalin turawa round (a zazzagaye) sai a soya sama sama. Sai a soya jajjagen attaruhu da albasa a zuba hanta da aka dafa/tafasa, a zuba carrot ,peas da duk k lambun da ake so. Sai a komai yai laushi a zuba dankalin, bayan minti 2 a fasa kwai a zuba a zuba slice onion in ya dahu sai a sauke. Ana cin shi haka ko da abinda ake so.

7-Potatoe croquetes: A dafa dankali 4 a daddaka shi sai a fasa kwai daya a sa a dama madara a zuba a sa gishiri kadan da garin masoro, sai a sa flour yadda zai yi kwari . Sai a yi ball din sa a tsoma a kwai, a sa a bread crumbs(garin bread) a soya a mai (deep frying).

8- A dafa dankali ba luguf ba a yanka shi cubes sai a zuba mai kadan a kasko da albasa ta soyu kadan sai a peas da carrots a soya. Sai a zuba dankalin da dandano da curry a juya. Sai a fasa kwai a kai a juya a barshi minti daya sai a sauke. Ana ci haka ko da bread.

9- Potatoe balls: A dafa dankali a daddaka shi ya marmashe, a zuba dakakken nama, attaruhu, albasa dandano a yanka dafaffen kwai in ana so. Sai a duddunkula shi a tsoma a kwai a sa a flour a soya.

10- A dafa dankalin turawa sama-sama sai a raba shi biyu a tsaye sai a daka nama dafaffe da attaruhu da albasa da dandano a sa a kan dankali daya a rufe da dayan a tsira tooth pick (tsinken sakace) a hade su da shi don kar su rabe. Sai a soya . Za a iya tsoma shi a kwai kafin a soya.

Zubaida isah✍🇳🇬
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts