NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

GAREKU MATA..... HADIN GYARAN NONO

GYARAN JIKI

Za mu fara da sinadaran gyaran mama,
wannan hadin na farko da zan rubuto
yana karawa mace girman nono kuma sam
ba ya faduwa. Ko da a ce tana shayarwa
ne idan har tana amfani da wannan hadin
sai dai mu ce Allah san barka.
Uwargida, ki nemi wadannan kayayyakin:
1). Farar shinkafa
2). Garin Alkama
3). Garin habbatus sauda
4). Garin Ayaba (Plantain).
5). Gyada mai malfa (mai zabo)
6). Aya
7). Madarar gari.
8). Zuma
Za ku bare bayan plantain sai a yanka shi,
a shanya ya bushe, sai a daka, a hada da
garin alkama da garin farar shinkafa, sai a
hada aya da gyadar a markada a tace
ruwan. Bayan nan, sai a dora kan wuta a
zuba garin Plantain da alkama da farar
shinkafar da muka hade a guri daya, sai
kuma ku zuba garin madara da zuma, ku
dama ya yi kauri sai a rika sha safe da
yamma.
Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati
biyu kafin yaye, kuma ba kya shayarwa, za
ki iya sha, sai ki tanadi rigar mama, wato
Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa
mamanki su tsaya sosai, ki rika sakawa. Ki
yi haka na tsawon sati biyu, da yardar
Allah za ki samu biyan bukata. Allah ya
tamake mu.
Idan kuma baki da halin siyan duka
wadannan kayayyakin da na ambata to
kina iya yin kunun alkama ki rika sha sau
biyu a rana, amma za ki rinka sa madarar
gari, wato kunun alkama da madara ke
nan. Ko kuma ki sami garin hulba, ki tafasa
ki rika gasa nonon da shi, sai kuma a shafa
man hulban a kan nonon a ga abin
mamaki sannan kuma a fasa kwan salwa a
shafawa nonon, kuma a fasa guda uku a
sha su danye. Insha Allahu za a dace.
Ga kuma gyaran jiki da fuska gaba daya
fata tayi laushi da shezi zaki tanadi ababe
kamar haka:
1. Man Zaitun
2. Lalle
3. Kur-kur
4. Madarar ruwa (peak)
Za ku hade wadannan kayan hadin guri
guda sai ku kwaba su ku shafe jikinku da
fuskar ku, za ku yi wannan hadin kafin ku
shiga wanka idan ya bushe a jikin ku sai
ku murje sannan sai ku shiga wanka,
wannan hadin ya na sa jiki yayi kyau da
sheki insha Allahu.
Za ku iyayin wannan ma wanda ake hada:
1. Kur-kur
2. Dilka
3. Zuma kwai
4. Lemon tsami
Za ku hade su a guri guda ku samu ruwan
ku kwaba kamar yadda ake kwaba lalle,
amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ku
shafe fuskanku, idan kuma har da jiki kuke
so, sai ku shafa harada jiki bayan awa daya
sai ku shiga wanka za k ga yadda jikinku
zai goge. Das da izinin Allah. Domin
wannna hadin shi ake kira Dalleliya.
Ga kuma wani hadin har wayan na gyanan
fatan jiki zaku tanadi:
1. Lalle
2. Kwaiduwar kwai 3
3. Manja cokali 3
4. Kur-kur
Sai ku kwaba su guri guda ku shafe jikinku
zuwa awa guda, sai ku yi wanka da ruwa
zalla sai ku jika duka da ruwan dumi ku
shafe jikin da ita sai ku kuma yin wanka.
Allah ya taimake mu.
Idan kuma gyaran fuska ku ke so sai ku
tanadi:
1. Dettol
2. Sabulun Ghana
3. Garin Zogale
4. Farar albasa.
Sai ku hade su guri guda ku kurba su a
turin ku mulmula ku rinka wanke fusku za
ku ga yadda fuskarku za ta y i kyau.
Wannan kuma hadin yanasa fuska ya yi
haske ya yi kyau da annuri ya kuma kore
kurajen fuska za’a tanadi abae kamar
haka: Bawon kankana sai a runka goge
guska da shi yana gyara fuska ya yi sumul.
Ga kuma wani hadin duk na gyaran fatar
jiki shi ma wannan hadi ne na musamman
wanda ya ke sa fatar mace ta zamo tana
tare da shauki da laushi kai har ma zaki ji
jikin ki yana wani damshi damshi wannan
hadi ne da yawanci amare ka wai ake yi
wa shi. Za ku tanadi ababen kamar haka:
1. Ayaba
2. Lemon tsami
3. Tataciyar madara
4. Kwai daya
Za ku sami ayaba mai kyau ku bare k
matse da hannuku, ko ku markada a
blenda ya yi laushi, sai ku zuba tataciyar
madara ku fasa kwai kamar guda daya
amma farin zaku zuba sai ku matse
lemoun tsami ku gauraye shi ku shafa a
jikin ku ya samu kamar tsayin awa daya,
sai uk yi wanka da ruwan zafi, idan har
kuka lazinci yin haka kamar kwana uku za
ku sha mamaki.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts