NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

FATE FATEN SHINKAFA.......

Abubuwan hadawaShinkafa
Alaiyaho da yakuwa (ki gyara ki yanka su, ki wanke da gishiri)
Albasa mai lawashi (ki yanka)
Maggi (ya danganta da irin dandano ki)
Tarugu (ki jajjaga)
Albasa (ki yanka)
Manja mai kyau (ki soya)
Gyadar miya zaki dakata (optional)
Dafaffafen nama ko kifi banda (ya danganta da irin wanda kike so)


Yanda ake hadawaDa farko ki sa tukunyanki akan wuta ki sa ruwa yanda zai isheki ki dafa shinkafar ki. Har ya danyi ruwa ruwa (tunda fate akace) Saiki wanke shinkafarki ki zuba a ciki ki barshi yayita tafasa har sai kinji ta fara laushi.
Sai ki dauko tarugu ki sa ki kawo maggi, nama ko kifi, curry, kayan kamshi da gishiri ki sa daidai dandano da zai miki.
Ki dauko manja ki sa, sai ki kawo ganyen lawashi ki zuba a ciki, daga karshe kuma ki dauko gyada ki zuba sai ki juya a hankali. Sannan ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin (amma ki na juyashi a hankali nadan wani lokaci) har sai komai ya nuna.


Sai ki sauke ki zuba a kwano ko plate. A ci dadi lafiya

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts