NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

CIKI DA GOYI.......
CIKI DA GOYO

Akan samu wassu mata suna shayarwa kuma a samu kwatsam sun samu juna biyu. Wannan! a Hausance shi ake kira ciki da goyo.

Wato mace ce bata gama yaye jaririn da take shayarwa ba sai ciki ya shiga.

Mafi yawan iyaye a daidai wannan lokocin hankalin su yana tashi ganin cewa yaro bai girma ba kuma a al'adance mace idan tana da juna bata shawayar wa.

Duk da cewa anfi samu cewa a akasarin mata masu shayarwa al’adarsu ma bata dawowa ballantana su samu wani cikin, wassu matan kuma al'adar su tana zuwa ko suna shayarwa.

ABIN TAMBAYA SHINE A LIKITANCE MACE MAI CIKI ZATA SHAYAR DA YARO KA A'A ???

A likitance mace mai goyo da ciki babu wani dalilin da zai sa a dauke jariri daga shan nono, saidai ko idan uwar batada isheshahen lafiya.

Idan mace batada isheshshen lafiya za'a iya dauke yaro daga shan nono amma da sharadin an tanada masa abinci masu gina jiki ( duk da komin kyeun abincin bazai kai ruwan nono ba )

A al’ada ce kawai akan cewa dan (Yaron) zai iya shanye ciki. Wanda hakan ba gaskiya bace.

A Karshe dai a likitance mace zata shayar da jariri alhalin tana dauke da ciki, domin mace mai shayarwa kan samar da madara yayin da take da juna biyu.

TO IDAN CIKI YAKAI WATA NAWA ZA'A DAUKE YARON DAGA NONO ??

koda mace za ta sake haihuwa alhali wanda ake shayarwa haryanzu baya karban wani abinci yadda ya dace, baza a dauke yaron daga nono ba, haka nan za'a hadasu kamar tagwaye aci gaba da shayarwa bayan an haihu.

Wannan shi ake kira tandem breastfeeding a
likitance, wanda kusan kamar shayar da ’yan biyu ne.

Abin da dai ake bukata ga uwar shi ne karin abinci masu gina jiki da sinadaran vitamin na kwayoyi na sha wadanda za su taimaka mata da abin da ke ciki.

Sai kuma ya kasance cewa shi wanda ake shayarwar kafin a samu wani juna biyun an riga an fara shi a kan abincin jarirai mai dan ruwa-ruwa kafin a zo daga bisani a yaye shi.

JAN HANKALI:

1- Macen da ta taba yin bari ( miscarriage ) kada tayarda taci gaba da shayawar duk sanda tasamu ciki yakamata taje asibity dan neman shawarwari.

2- Macen da ta taba haihuwa bakwaini (Premature labour ) itama kada taci gaba taje asibity .

3- Macen da take zubar da jini ( bleeding ) itama kada taci gaba da shayarwa taje asibity .

Rubutawa : Zannah Mustapha Wakil

Daga: Whatsapp Health Section
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts