NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

AMFANIN NAMIJIN OGA GA LAFIYAR DAN ADAM

Namijin goro dai wani nau'i ne na goro wanda akasari ake amfani da shi a kasashen Africa. Turawa na kiranshi da suna "bitter kola" Yorubawa sun kiraye shi da suna "orogbo", Inyamurai kuma na kiranshi da suna "akiilu".Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana namijin goro da antibiotics mai matukar amfani ga rayuwar bil'adama. A nazari da aka gudanar daban-daban a sassan Africa da ma na Turai, an tabbatar da namijin goro na da amfani kamar haka:1. Kamar yadda kwararriya a fanin nazarce-nazarce a sashin kiwon lafiya na Nigeria Natural Medicine Development Agency (NNMDA), Mrs. Chinyere Nwokeke ta tabbatar da cewa, namijin goro yana taimakawa masu dauke da cutar HIV ko kanjamau ta hanyar rage radadi da gubar da cutar ta HIV take dauke da shi saboda sinadarin "antibacterial" da kuma chemical na "Saponin" da yake cikin ta.2. A wani nazari da masana suka gudanar a sashin horar da likitoci na jami'ar tarayya dake Lagos, masanan sun bayyana kamar yadda aka wallafa a mujallar "Middle East African Journal of Opthamology" cewa, namijin goro na kashe cutar Glaucoma wacce take lalata idanun bil'adama.3. Har ila yau, masana a fannin kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, namijin goro na maganin cutar cizon sauro wace ake kira da "malaria" saboda sinadarin "kolaviron" da ke cikin ta.4. kwararru a fannin nazarce-nazarce a sashin kiwon lafiya na jami'ar Obafemi Awolowo dake Ile'ifi, sun tabbatar da cewa, namijin goro na magance amosalin gabbai (arthritis). Har ila yau, a nashi jawabi Dr. Olayinka O. Adegbehingbe ya jaddada hakan a wani nazari da ya gabatar kuma aka wallafa a mujallar, issue of the Journal of Orthopaedic Surgery and Research, a watan Juli na shekarar 2008. Kwararren ya tabbatar da cewa namijin goro na matukar magance cutar gabobin jikin.5. Har ila yau, an tabbatar da cewa namijin goro na karawa maza kurzahari wajen gabatar da sunnan aure.

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts