NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

ADDININMU NASIHA 2.......FADAKARWAFadakarwa a musulunci
YIN SALLAH AKAN LOKACI: JINKIRTA SALLAH IDAN BA TARE DA WANI UZURI BA HARAMUN NE.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ ­­♠♠
A rayuwa Sallah itace kan gaba. Ita ce farkon abin da za a yi mana hisabi a kanta,amma haryanzu wasu daga cikinmu basa bata Mahimmanci. Manzon Allah SAW don ya nuna mana darasi da mahimmancin Sallah, baya jinkirta lokacin Sallah, ko da kuwa yanada larura ne. Amma mu Allah ya kawo mu wani zamani wanda gashi Allah ya wadata mu da lafiya amma bama amfani da wannan damar wajan bauta masa. Saboda haka wlh jinkirta Sallah idan ba tare da wani uzuri ba haramun ne.
Kuma irin wadannan abubuwa a rayuwarmu ga sunan jingim suna faruwa. Wani yanzu saboda taro, taro da aka shirya na Siyasa ne, ko na Office, ko na gwamnati ne, zaku ga anzo anyi Azahar ta zo ta wuce, La'asar,Maghriba duk sun wuce,mutum yana sane duk yaki yinsu akan lokaci, sai daga baya kuma kaga mutum yazo zai yi Sallah kuma sai kaji mutum ya fara ce "Astaghfirullah ­ ­... Astaghfirullah. ­­.. Ai wannan ma rainin hankali ne wallahi, mun yarda mu mubi mahaluki dan uwanmu mu sabawa Ubangijinmu da gangan,(Duk mun manta da wadancan Azabobi da Allah ya tanadar ga masu jinkirta Sallah, balle kuma ga wadanda basu ma damuda Sallar ba, balle suyi tunanin yinta.)
Mun qi yin Sallah akan lokacinta don amfanin duniya wanda muke ganin idan bamu halarci wannan taro ba zamu yi wata Asara, to wlh da zaka tashin(ana wannan taro kaje kayi Sallar) a rage maka wani abun tunda dan Allah kayi, sai kaga Allah yayi maka Sauyi mafi Alkhairi, mafi nutsuwa, mafi faqin ciki da kwanciyar hankali a rayuwarka...
Dan ALLAH, Dan ANNABI 'yan uwana ya kamata mun yiwa kanmu karatun tanutsu. Idan yanzu anan duniya bamu bautawa Ubangijin da ya halicce mu bato a ina zamu bauta masa...LAHIRA?? ­­ To wallahi tun wuri mu sauya tunani don yaudarar kanmu muke. Ba wanda yasan ranar mutuwarsa... pls share
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts