NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

SAI KUNNIN MAIGIDANA YAYI MOTSI

SAI KUNNIN MAIGIDANA YAYI MOTSI //4

WAINAR NAMA DA KWAI DA DANKALI

INGREDIENTS:
•Nama yanka 10
•kwai guda 5
•Dankalin turawa guda 2
•Mai
•Maggi/Gishiri/curry/onga chicken & classic
•Tattasai/tarugu/albasa.

PROCEDURE:
Farko dai ki tafasa naman ki, idan ya tafasu sai ki daka shi a turmi mai kyau ko ki niqa a blender, sai ki sami roba ko kwano ki fasa kwanki ki zuba a ciki, kisa maggi, gishiri dan kadan, onga classic da chicken, shi ma dan kadan, kisa curry dan dai-dai, ki yanka albasa 'yan 'kanana-'kanana yadda zai ji sosai.

Daga nan sai ki jajjaga attarugu guda uku, tattasai biyu da albasa kadan, ki jajjaga shi sosai, ki zuba kayan miyan nan a cikin kwan, sai ki fere dankalin ki guda biyu, amma kada ki dafa, ki kankare shi a cikin kwai dinnan, sai ki dauko naman ki ki zuba, ki juya shi sosai ya hade, idan kika ga ruwan kwan babu yawa zaki iya fasawa a wani kwano ki kada ki qara.

Sai ki dauko frying pan (tukunyan suya) ki sa a wuta, soya shi zaki yi kamar yadda zaki soya kwai, amma kada ki cika wuta, daga nan sai ki rinka debowa kina soyawa, idan bayan ya soyu sai ki kifa kamar yadda ake kifa meat pie, haka zaki yi ta soyawa a hankali, kina juya bayan shi kina juya gaban shi, har ki gama. Zaki ga ya bada shape din meat pie.

Akwai dadi sosai, zaki iya yin shi a sha ruwa da shi lokacin azumi, ko kuma ki yi shi bayan an gama dinner sai a daura a sama.

Daga Sister Sadeeya Lawal Abubakar.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts