NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

MALAM AMINU IBRAHIM DAURAWA

TUN RAN GINI TUN RAN ZANE 

MANZON ALLAH SAW YACE : DUK ABIN HAIHUWA, ANA HAIHUWARSA AKAN FIDRA TA ADDINI, IYAYE SU KE YAHUDANTAR DA SHI,  KO SU NASARANTAR DA SHI, KO SU MAGUZANTAR  DA SHI.
BUKHARI DA MUSLUM. 

IDAN KAGA YARO DA AL'ADUN YAHUDAWA, KO MAGUZAWA KO NASARA. 
DAGA IRIN TARBIYYAR CE GURBATACCIYA DA YA SAMU DAGA MAHAIFANSA,  KO DAGA SAKACIN MAHAIFANSA.

GA ABUBUWA TARA, DA SU KE KARE YARO DAGA FADAWA HALAKA IDAN AN GINA SHI AKAI. 
NA DAYA, IMANI DA INGATACCIYAR AKIDA. 
NA BIYU, IBADA GA ALLAH KAMAR SALLAH AZUMI TUN YANA YARO. 
NA UKU HALAYE NA KWARAI KAMAR GASKIYA DA KUNYA DA AMANA DA MUTUNCI 
NA HUDU: ILMI NA ADDINI DA ZAMANI 
NA BIYAR : KULA DA LAFIYA DA NISANTAR KAYAN MAYE 
NA SHIDA : ZAMANTAKEWA, GIRMAMA MANYA DA TAUSAYAWA KANANA, DA BAWA DUKKAN MAI HAKKI, HAKKINSA. 
NA BAKWAI: KOYA MASA SANAA DA AIKIN YI. DOMIN YA DOGARA DA KANSA. 
NA TAKWAS:  NUNA MASA ILLAR ZINA DA LUWADI DA MADIGO, SA DUKKAN MU'AMALA MAI MAI MUNI. 
NA TARA:  ADDUA, TA NEMAN KARIYA DA TSARI DAGA FARMAKIN SHEDAN. 

ALLAH KA BAMU YAYA MASU ALBARKA DA TARBIYYA.

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts