NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

MAGANIN ULCER NA SADIDAN


MAGANIN CIWON ULCER (GYAMBON CIKI

. / 05-06-2018

Yan uwa masu daraja da daukaka ganin yadda Azumi ya gabato wanda muke saran gobe ko jibi za a tashi da shi yasa naga ya dace in dan bada gudunmawa ga masu fama da wannan lalura don naga wasu har ajiye Azumi sukeyi saboda wannan lalura ina fatan Allah ya basu lafiya

Yan uwa wanda Allah ya jarabceshi da wannan lalura yayi kokarin ya kiyaye wasu abubuwa
-shan sigari da duk wani nau'in abubuwa da suka shafi hayaki da kan iya jawo cuta
-shan magunguna barkatai ba bisa ka'ida ba
-shan abubuwa masu yaji da zasu jawo radadin ciki da sauran duk wani abu da kan iya jawo cutar

ABUBUWAN DA KAN TAIMAKA WAJEN MAGANCE CIWON ULCER

-habbatus sauda'a
-hulba
-karas
-zogale
-tafarnuwa
-ayaba
-kwakwa
-zuma
-kabeji da sauran wasu abubwa da kan iya taimakawa wajen magance cutar

MAGANIN CIWON ULCER

Wanda yake fama da wannan lalura sai ya jarabta daya daga cikin wadannan hanyoyi insha Allahu zai samu lafiya da yardar Ubangiji

- A samo ayaba a yayyanka a shanya a rana in ya bushe sai a nike a rika diban garin cokali 2 a hada da zuma cokali guda ana sha safe da yamma

- A dafa yayan hulba cokali 2 ana sha da zuma dan kadan ko kuma a hada garin hulba ana sha da madara safe da yamma

- A dafa ganyen zogale ana sha da Zuma safe da yamma

- A rika cin tafarnuwa guda 3 ko 2 kullm bayan anci sai asha ruwa Kofi guda

- A samo garin habba da hulba a had a da zuma ana shan cokali guda da safe kafin aci komai

Muna fatan Allah s.w.t ya bamu lafiya

M.A 08
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts