NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

KA SAN JIKINKA: Makomar Abinci A Cikin Mutum (2)


Satin da ya wuce, mun tsaya ne akan tafiyar abinci cikin karamin hanji. A inda nake cewa Ana wuce sashen farko na karamin hanji, sai a ci karo da hamshakiyar gabar nan, daga bangaren dama wato hanta.

Hanta ce ke hada wani sinadarin mai daci sannan ta adana shi a cikin wata karamar jaka dake kasan ta. Shi wannan ruwa mai daci, shi ake kira “bile”. Jakar da kuma aka adana shi ita ake kira “gall bladder” ko kuma madaaciya da hausa.

Ana zubo wannan ruwa cikin abinci matukar cewa acikin abincin akwai ajin abinci mai dauke da kitse (fat). Aikin wannan ruwan madaaciya shi ne farfasa kitse zuwa ya koma kamar tsaki.Mafi rinjayen aikin farfasa abinci, narka shi da zuke amfanin da ke cikin sa, na faruwa ne a sashen farko na karamin hanji. A cikin ragowar sashen, kawai ragowa ne da dan abin da ba’a rasa ba na abin da bai Riga ya narke ba.

Abincin da ya bar sashen farko na karamin hanji baya shiga cikin hanta; ita abin da ke shiga cikin ta shi ne jini mai dauke da sindaran amfanin da aka zuke a cikin abinci.

Hanyoyin jini suna da matukar yawa a jiki kuma suna da alaka da juna. Saboda haka, hanyoyin jinin da suka zuko abubuwan amfani daga abinci suna da hanya kai tsaye zuwa bututun jini na hanta. Zagayawar jini daga karamin hanji zuwa hanta shi ake kira da “portal circulation”.Lokacin da abinci yaje sashen karamin hanji na karshe, sinadaran stati da ake samu a ajin abinci mai bada kuzari (carbohydrates) duk sun koma ainihin jigo mai bada kuzarin wato “glucose”. Idan za’a adana shi a jiki domin amfani da shi nan gaba, sai a mayar dashi “glycogen”.

Haka kuma a sashen karshen dai, na karamin hanji, za’a iya samun ragowar abincin da bai gama narkewa ba, musamman kitse. A wannan gaba, madaciya zata zubo ruwan ta, ita ma matsarmama zata zubo nata.

Amma a madadin sai an bi doguwar hanya, wato hanyoyin jinin dake kasan karamin hanjin su zuke shi, sai a tura wannan ragowar sinadaran abinci cikin ruwan da ke share kwalbatoci na jiki.

Shi wannan ruwa ana kiran sa “lymph”, hanyoyin tafiyar sa kuma ana kiran su da “lymph bessels”. Lymph yana aiki kuma wajen bada kaariya ga barin yaduwar kwayoyin cuta a jiki. Hanyoyin “lymph bessels” Zasu dauki wannan ragowa su mayar dashi cikin jini domin ayi amfani dashi

Daga nan, duk abin da ba’a zuke shi ba, to jiki baya bukatar sa, sai a wuce da ragowar abincin cikin babban hanji. Aikin babban hanji ne ya dinga zuke ruwan da ke cikin wannan dusar abinci. Yadda abin yake, shi ne: babban hanji yana hana abinci ya tafi da sauri a cikin sa, ta haka ne yake samu ya zuke mafi yawan ruwan da ke cikin sa.Wani lokacin abinci na wucewa da sauri ta cikin babban hanji, kunga kenan ba zai samu damar zuke mafi yawan ruwan dake cikin dusar abinci ba a wannan yanayi. Mai zai faru? Gudawa ce zata faru. Kuma abin da yasa take sa raunin jiki shine mutum ya zubar da ruwan da jikin sa ke bukata wanda babban hanji bai zuke ba.

Lokacin da dusar abincin taje tsakiyar babban hanji, mafi yawan amfanin da kuma ruwan dake cikin sa, an riga an zuke su. Kwayoyin halittar dake cikin babban hanji, suna zubo da wata majina mai mataukar amfani.

Ita majinar tana hade datti, da dusar abinci waje guda, tana hana bangon babban hanji karcewa daga ciki yayin shigewar datti da dusar abinci ta cikin sa. Sannan tana hana acid din da ke cikin dusar abinci ta illatar da bangon babban hanji.Yana da kyau mu san cewa kaso casa’in da biyar na abinci, jiki ne ke zuke shi. Sannan kuma shi bayan gari ba zallar dusar abinci bane mara amfani, akwai sandararrun sindarai da suka gama aikin su (wanda tumbi, matsarmama, da madaciya suka feso). Sannan akwai kwayoyin halittu na bacteria.

Daga nan dusar abinci zata karaso ya zuwa dubura wato “rectum”. A cikin baabban hanji akwai kwayoyin bacteria wadanda ke taimakawa wajen hada wannan datti da dusar abinci waje guda.

Kwayoyin bacteria ne ke sanya bayan gari yayi doyi, duk da cewa ya danganta da yawan su a cikin babban hanji da kuma irin abincin da mutum ke ci. Idan mutum yana da su da yawa, to warin bayan garin sa zai fi na wanda bashi da su da yawa.

Haka ma idan an saake cin abinci, wadannan hanyoyi jiki yake bi domin ya tabbatar an yi abin da ya dace. Wannan shi ne abin da zan iya fada game da makomar abinci a cikin mutum.Mu hadu a wani satin da Yardar Mai Duka
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts