NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Ka San Jikinka: Makomar Abinci A Cikin Mutum


Yau idan Sarkin ya so, zan fara bayani kan makomar abinci a ciki, tun daga abubuwan da suke faruwa ga abinci a baki, har ya zuwa dubura.

Narkar da abinci da markada shi yana farawa ne tun daga baki. Yayin da kasa, ko kika sa laumar abinci a bakin ki, yawun baki shi zai fara yi masa maraba. Kamar yadda na fada a baya, a fuska akwai tsokoki da yawa, kuma anyi musu aji guda 2.

Akwai ajin tsokoki masu taimakawa wajen tauna; ana cewa dasu “muscles of mastication”, Akwai kuma masu nuna halin da zuciya take ciki: sana cewa dasu “muscles of facial edpression.

To da zarar abinci ya shiga baki, bayan yawu yayi masa maraba, sai tsokoki masu taimakawa wajen tauna su fara jujjuya abincin dama da hagu, sama da kasa, su na tabbatar da abincin a tsakanin turmin daka, kuma kashi mafi kwari, wato hakora.

A nan, ya danganta da ajin abincin da mutum yake ci a daidai lokacin; idan ajin masu gina jiki ne. Wato “proteins”, sai a ciki ne za a faara faffasa su, ware su da kuma sarrafa su, abin da a turance ake kira “metabolism”. Idan kuwa abinci a ajin masu bada kuzari yake wto “carbohydrates” , to tun a baki za a faara farfasa shi.Za a dagargaza abinci ya zuwa matakin da idan kuka kalli abinci za ku ga kamar an darza shi. Wannan darza ita bature yake kira “bolus” daga nan kuma sai a hadiye bolus izuwa makogwaro

Makogwaro yana. Da hanyoyi guda biyu. Akwai hanyar iska, da kuma ta ruwa da abinci. Idan abinci ya taho, sai hanyar iskar ta rufe ita kuma ta abinci ta bude. A lokacin da mutum ke magana, marufin hanyar iska yana budewa ne, shi yasa ba’ a so mutum yana cin abinci yana magana; saboda abinci zai iya kuskurewa ya shiga hhanyar iska, daga nan sai kwarewa, da taari da sauran su.

Daga nan abincin zai biyo wani tsukakken bututu wanda ya sadar da baaki zuwa tumbi wato “stomach”. Shi wannan bututu dake a wuya, Shi ake kira da “oesophagus”. Baya barin abinci ya wuce da gudu ta cikin sa.Shi yasa idan mutum ya cunkusa abici da yawa a bakin sa sannan yayI yunkurin hadiye Shi nan taake, Zai ji a jikin sa! Meyasa? Saboda ya kary dokar duniyar cikin jikin sa.

A karshen wannan butu wato oesophagus, ake samun tumbi$ tumbi Shi ne mai adana abinci na wucin gaadi, kimani awa biyu zuwa uku kafin abincin ya fita Daga cikin sa. A wannan gaba, abincin sunan sa “chyme” a turance.

A cikin tumbi akwai ruwan acid da ake kira “hydrochloric acid”. Aikin wannan acid din yana da yawa amma kadan Daga ciki Shi ne kaara dagargaza abinci da kuma ware su daki daki.

Bayan acid dinnan, tumbi na da sinadaran “hormones” da ke taimaka wa wajen narkar da abinci. Shi wannan acid yana da karfin gaske, wanda da zaaki saka reza a cikin sa, zata narke.

Bayan awa 2 zuwa 3, abincin zai bar cikin tumbi, ya shiga karamin hanji. A cikin karamin hanji ma, akwai sindarai masu tarin yawa da ke sarrafa abincin. Shi karamin hanji yana da sashe uku ne. A sashen farko daga bangaren hadu, da akwai matsarmama da take aiki muhimmi.A na Kiran matsarmama da “pancreas” kuma tana da wani ruwa da take fester ta cikin bututun ta, wanda kofar sa ta bude har cikin sashen farko na karamin hanji. Wannan ruwa yana da muhimmaci kwarai domin yana narkarwa da sarrafa ajin abinci guda uku.

A karkashin shimfidar karamin hanji, akwai hanyoyin jini masu yawa wadanda jini ke kai kawo a cikin su. Aikin su shi ne zuke amfanin da ke cikin abinci yayin da abincin ke gudanar da tafiyar sa a cikin karamin hanji.

A na wuce sashen farko na karamin hanji, sai a ci karo da hamshakiyar gabar nan, daga bangaren dama wato hanta. Abincin da ya bar sashen farko na karamin hanji baya shiga cikin hanta; ita abin da ke shiga cikin ta shi ne jini mai dauke da sindaran amfanin da aka zuke a cikin abinci.

Mu hadu a wani satin domin ci gaban wannan bayani da Yardar Mai Duka.
Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts