NXBpuAZjdZs2pK1hTXWNbChD8gXUeLhCEbFxYYDh

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

HADADDUN LEMUKAN ZAMANI

HADADDUN LEMUKAN ZAMANI

(1) LEMON DANKALI
DankalinHausa,Madara,Sugar,Yadda Za ki hada shi ne: zaki sami dankalinki na Hausa sai ki fere shi, ki yanyanka shi sannan sai ki markade shi sannan sai ki kawo Suganki sai ki zuba yadda kike so, sannan sai ki zuba madara ta ruwa za ki iya sa falavor in har kina so.

2) LEMON SHINKAFA
Danyer Shinkafa,Dankalin Hausa,Sugar,Flavour,Citta
Yadda za a hada shi idan kika sami dankalinki na Hausa, bayan kin fere shi sai ki sami danyar shinkafarki ita ma bayan kin jika ta ta jiku sannan sai ki sa 'yar Cittarki da dan kanunfari shi ma sai ki zuba kadan. Sannan sai kikawo Wannan danyan dankalin wanda kika fare shi sannan kika yayyanka shi kanana sai ki markade Sai ki hada a cikin jikakkiyar shinkafarki sai ki hada ki markade. Bayan kin tace da rariya mai laushi,sai ki kawo sugarki wanda daman na rigaya na gaya miki ana so ki dafa shi sai ki zuba daidai yadda kike so.Sannan sai ki zuba flavour a cinki sai ki sanya a gidan sanyi.

3) LEMON KANKANA DA APPLE
1. Kankana 2.Apple 3.Sugar 4.Flavour 5. Zuma Yadda za a hada shi shi ne, idan kika sami kankanar ki sai ki fere ta, Sannan sai ki sa apple dinki mai jan baya sai ki hada ki markade. Bayan kin fere kankanarki,ki hada su,Sannan sai ki zo kikawo Sugarki ki zuba daidai da yadda kike so Sannan sai kawo flavour dinki Sai zuba. Sannan Sai ki adana shi a gidan sanyi, domin sanyaya zuciyarmaigidanki.

4) LEMON ZOGALE 1. Zogale 2. Na'ana 3. Sugar 4. Citta 5. Kaninfari,,, Yadda za a hada shi idan kika sami zogalenki dan dama,Sannan za ki sami 'yar na'anarki sai ki zuba 'yar kadan.Bayan kin gyara su kin wanke su sai ki markade su, Sannan Sai ki tace su,sai ki kawo sugarki ki zuba daidai bukatarki,Sannan sai ki kawo flavour dinki Sai ki zuba, Cittarki dama da kanunfarinki a cikin markade za ki sanya su don haka bayan kin markade kin sanya Sugarki,Sannan kin kawo wannan flavour kin zuba, sai ki sanya shi a gidan sanyi.
5) LEMON MADARA DA DABINO,, 1.Dabino 2. Madara ta ruwa 3. Dankalin Hausa 4. Sugar 5. Citta da Kaninfari, Yadda za a hada shi ne idan kika sami dabinonki kika bare shi sai ki jika shi Sannan ki fere Dankalin ki na Hausa Sannan sai ki yayyanka dankalinki kanana, bayan kin fere shi sai ki hada dabinonki tara da dankalinki sai ki markade su. Za ki sanya Citta da Kaninfari sai hada ki markade. Bayan kin tace sai ki kawo sugarki sai ki zuba daidai bukatarki, Sannan sai ki kawo flavour dinki Sai ki zuba sai ki sanya lemonki a cikin sanyi.

6) LEMON KINDIRMO (NONO) DA MADARA,,1. Kindirmo (nono) 2. Madara 3.Sugar 4. Dankali Yadda za a hada shi ne idan kika samu dankalinki za ki fere shi Sannan Sai ki markade shi. Sai ki kawo nonon nan Sai ki hada a cikin ruwan tataccen dankalinki, Sannan Sai ki hada bayan ki sake tacewa Sannan Sai ki kawo sugarki sai ki zuba daidai bukatarki sai ki zuba dan flavour dinki domin lemonki ya yi kamshi da ban sha'awa. This dish is a Coastal E/African delicacy that is a loved by almost every family up and down the East Coast, from Mombasa, to Malindi, Lamu and all the way to Zanzibar! A delicious smoky flavourful grilled fish which is then coated with a rich, thick and creamy tamarind-flavoured coconut sauce.This dish is particularly enjoyable with Coconut Rice but can also be had with Mandazi, or Naan and maybe a side of spinach. Once you try this dish, it will definitely count as one of your favourite exotic seafood meals!! YUM!!

Serves 4

Related Posts
Mr. Naxee
I Am Nazeer Naxee CEO/Founder Of ArewaFresh Blog. Thank You!

Related Posts