💐💐💐 *SIRRIN YA MACE GROUP *💐💐💐
*admin maijidda bello*✍️
FILLIN GIRKE GIRKE 🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘🥘
*FARFESUN TALIYAR HAUSA DA NAMAN KAZA *😋
Abubuwan da za a bukata
•Bata cokula biyu
• Ganyen kori
• Yankakkiyar karas
• Yankakkiyar albasa kamar rabin kofi
•Ganyen ‘thyme’
• Kayan kamshi
• Kowace magi wadda aka yi da dandanon kaza
• Kaza daya
• Taliyar hausa ko ta ‘indomie’
• Romon kaza
• Barkono
• Garin tafarnuwa
Hadi
A wanke kaza sannan a zuba mata yankakkiyar albasa da gishiri kadan har sai ta nuna sosai ta yi laushi. Sannan a dora tukunya a wuta a narkar da bata sannan a zuba yankakken karas da yankakkiyar albasa da yankakken lawashi a dan soya sama-sama. Sannan a zuba ganyen ‘thyme’ da magin mai dandanon kaza.😋
A debo romon kaza sannan a zuba a ciki har sai ya tafasa sannan a zuba garin tafarnuwa da dakakken barkono sannan a rage wuta sai a zuba taliyar hausa a ciki sannan a rufe na tsawon minti 20, sannan a sauke shi da romo-romonsa ana sha ana taunar namar kaza da taliya.
*admin maijidda bello *✍️✔️